Muna Kokarin Mu Yanke Huldar Kudi da Ksar Faransa, Mu Koma Naira, Inji Mohamed Bazoum Na Nijar

Muna Kokarin Mu Yanke Huldar Kudi da Ksar Faransa, Mu Koma Naira, Inji Mohamed Bazoum Na Nijar

  • Shugaban jamhuriyar Nijar ya bayyana cewa, kasarsa za ta yi amfani da kudaden Naira a nan gaba
  • Ya bayyana hakan ne tare da bayyana shirin da ECOWAS ke yi na kawo sauyi a tsarin kudaden Afrika
  • Ya kuma bayyana cewa, kasarsa za ta yanke alakar kudi da kasar Faransa saboda wasu dalilai na siyasa

Fadar shugaban Nijar - Shugaban jamhuriyar Nijar ya bayyana cewa, kasarsa za ta daina amfani da kudaden Faransa nan ba da jimawa ba tare da duba yiwuwar amfani da Naira ta Najeriya.

Ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ya yi da shugaban sashen Hausa na BBC a wata hira ta musamman da suka yi.

Ya bayyana cewa, duk da kudin Naira na Najeriya na da wasu tsarabe-tsarabe na siyasa da kasarsa bata gamsu dasu ba, amma akwai yiwuwar a gaba a daidaita kasar ta karbe su.

Kara karanta wannan

Yawaita Zuwa Turai: Tinubu zama zai yi ya mulki Najeiya, inji hadiminsa

Mohamed Bazoum ya ce Nijar za ta yi amfani da Naira
Mohamed Bazoum na Nijar da Muhammadu Buhari na Najeriya | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Ya kuma bayyana cewa, kudin yanzu na Faransa da Nijar ke amfani dasu na da wasu fa’idojin, amma duk da haka jamhuriyar za ta yanke hulda da kudaden da ba na Afrika ba saboda dalilai.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Za mu so yin amfani da Naira

Da yake bayani game da tsarin kudin Eco a yankin Afrika ta Yamma da ake kokarin yi, shugaban na Nijar ya ce:

“Muna son a samu ya zama kudinmu guda ne da Najeriya saboda babbar kasa ce da iyakanmu wanda rashin amfani da kudi iri daya yana da illa ga tattalin arzikinmu.
“Mun fi son haka, amma ba za mu kaurace ma Sefa yau mu koma Naira ba saboda bamu yarda da siyasar Najeriya da take amfani da ita a kan kudi ba.
“Muna ganinta (Naira) da laifi mai yawa. Kuma muna ganin amfanin Sefa da yadda aka tsara ta, tana da abubuwa masu inganci.”

Kara karanta wannan

Kaico: Matashi Ya Aika Mahaifiyarsa Kiyama Saboda Sabanin da Suka Samu a Kan ₦10,000

Za a samu kudi na ECOWAS

Ya kuma bayyana cewa, gamayyar kasashen Afrika ta Yamma a ECOWAS za ta tattauna kan batun da ke da alaka da sauya kudin nahiyar.

Ya kara da cewa:

“Tattaunawar da za mu yi cikin ECOWAS, zai ba mu damar sanin wacce irin siyasa ce za mu gudanar domin ta yi mana amfani.
“Mu muna cikin Sefa, Insha Allahu za mu yi gwagwarmaya don sauya mata suna, za mu yi gwagwarmar yanke ‘yar alakarmu da Faransa, kenan za mu samu kudi na mu anna ECOWAS na mu mu kadai."

Idan baku manta ba, an samu tsaiko a lokacin da aka sauya kudi a Najeriya, inda wasu ‘yan Najeriya suka fara amfani da Sefa ta Nijar a bana a wasu jihohin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel