Yanzu-Yanzu: Hawaye Sun Kwaranya Yayin Da Babban Basarake Ya Riga Mu Gidan Gaskiya Yana da Shekara 87
- Babban basarake mai sarautar Onidimu na ƙasar Idimu, Oba Azeez Dada Aluko Olugoke, ya koma ga mahaliccinsa yana da shekara 87 a duniya
- Hukumar Egbe Idimu LCDA, itace ta tabbatar da komawar basaraken ga mahaliccinsa ranar Lahadi, 14 ga watan Mayu cikin wata sanarwa
- Shugaban hukumar Egbe Idimu LCDA, Sanyaolu Olowoopejo, ya bayyana cewa Oba Olugoke ya yi bakwana da duniya a ranar Lahadi, bayan ƴar gajeruwar rashin lafiya
Jihar Legas - Rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar da cewa shugaban hukumar Egbe Idimu LCDA, ya sanar da mutuwar Onidimu na ƙasar Idimu, Oba Azeez Dada Aluko Olugoke.
A cikin wata sanarwa ranar Lahadi, 14 ga watan Mayun 2023, wacce shugaban hukumar Egbe Idimu LCDA, Sanyaolu Olowoopejo, ya fitar, ya bayyana cewa Oba Olugoke, ya mutu ne da safiyar ranar Lahadi bayan yayi fama da ƴar gajeruwar rashin lafiya.
An sanar da lokacin binne basaraken
Olowoopejo ya kuma cigaba da cewa, iyalan mamacin za su sanar da lokacin binne shi nan ba da daɗewa ba.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ya yi wa gidan sarautar ta'aziyar rashin da suka yi tare da al'ummar garin Idimu bisa wannan babban rashi na basaraken.
Olowoopejo ya bayyana marigayin a matsayin, mutum mai son zaman lafiya, wanda ya ke son cigaban al'ummar da ya ke mulka.
Idimu yana ɗaya daga cikin garuruwan da ke da yawan jama'a a ƙaramar hukumar Alimosho ta jihar Legas, ƙaramar hukumar da ta fi kowacce yawan jama'a a jihar Legas.
Mutuwar basaraken dai babban rashi ne ga al'ummar da ya ke mulka da kuma mutanen jihar Legas gaba ɗaya.
Allah Sarki Wani Babban Basarake Ya Hadu Da Ajalinsa a Maboyar Masu Garkuwa Da Mutane
A wani labarin na daban kuma, an shiga jimami da takaici bayan wani babban basarake, ya gamu da ajalinsa a hannun miyagun ƴan bindigan, da suka yi awon gaba da shi a jihar Kogi.
Cif David Obadofin, basaraken Aghara a ƙaramar hukumar Kabba-Bunu ta jihar Kogi, ya yi bankwana da duniyar nan ne a hannun ƴan bindiga, kwanaki 12 bayan sun yi garkuwa da shi.
Basaraken ya ce ga garin ku nan ne a hannun miyagun ƴan bindigan bayan sun azabtar da shi iya azabtarwa.
Asali: Legit.ng