Kotu Ta Tura Babban Basarake a Jihar Ondo Gidan Gyaran Hali Na Shekara 10

Kotu Ta Tura Babban Basarake a Jihar Ondo Gidan Gyaran Hali Na Shekara 10

  • Wata kotu ta tura wani basarake a jihar Ondo magarkama bisa zargin rushe ginin wata coci ba bisa ƙa'ida ba
  • Basaraken na ƙauyen Ode, ya rushe katantar wata coci ne sannan ya lalata bishiyoyin dabino da amfani gona na cocin
  • Kotun majistaren ta tura shi gidan gyaran hali har na tsawon shekara 10, amma ta ba shi zaɓin biyan diyya

Jihar Ondo - Wata kotun majistare a jihar Ondo ta tura basaraken ƙauyen Ode a ƙaramar hukumar Akure ta Arewa, Oba Adewale Boboye, gidan gyaran hali, bisa laifin rusa wani gini, lalata bishiyoyi da amfanin gona, ba bisa ƙa'ida.

The Punch tace ginin da ya rusa mallakin cocin Apostolic ce, wacce ke akan titin hanyar Ado Ekiti, a yankin Igoba, Akure.

Kotu ta tura basarake a jihar Ondo gidan gyaran hali
Basaraken ƙauyen Ode, Oba Adewale Boboye Hoto: Royalnews.com
Asali: UGC

An gurfanar da shi gaban kotun ne kan tuhumomi shida waɗanda suka ginu akan aikata ɓarna.

Kara karanta wannan

Ta Fasu An Ji: An Fallasa Abinda Tinubu da Gwamna Wike Su Ke Kulla Wa Atiku Abubakar a Kotu

Mai shigar da ƙara, Ajiboye Babatunde, ya gayawa kotun cewa, basaraken da wasu a tsohuwar cocin Pastorate and Laity of The Apostolic, Najeriya, sun haɗa baki domin aikata laifin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kuma gayawa kotun cewa basaraken ya rushe katangar cocin wacce darajarta ta kai N1m, bishiyoyin dabino da amfanin gona wanda darajar su ta kai N5m, da kuma allon cocin, cewar rahoton Daily Post.

Basaraken ya nemi sassauci

Sai dai basaraken, ta hannun lauyansa Adeola Kayode, ya musanta zarge-zargen da ake masa, inda ya buƙaci kotun da ta yi rangwame wajen yanke hukuncinta.

Da ta ke yanke hukuncinta, alƙaliyar kotun, majistare Bukola Ojo, ta yanke masa hukuncin shekara 10 a gidan kaso, bayan ta same shi da laifi kan tuhumar da ake masa.

Kotun ta kuma yanke a biya diyyar N5m ga mai shigar da ƙara, bisa rusa katangar da lalata bishiyoyin dabinon da sauran amfanin gonan.

Kara karanta wannan

Majalisa Ta 10: Dalili 1 Rak da Yasa Tinubu da APC Suka Zabi Akpabio da Abbas, Shettima Ya Tona Gaskiya

Mai shari'ar ta bayyana cewa, idan basaraken zai iya biyan diyyar, za a soke hukuncin tura shi gidan gyaran hali.

Yan Bindiga Sun Sace Shugaban Jam'iyyar APC a Jihar Imo

A wani rahoton na daban kuma ƴan bindiga sun sace shugaban jam'iyyar APC a jihar Imo. Ƴan bindigan sun bi shi har gida sannan suka yi awon gaba da shi.

Ƴan bindigan waɗanda ake kyautata zaton makiyaya ne, sun sace Chinedu Eleliam, wanda shine shugaban jam'iyyar APC a ƙauyen Umuorugo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng