Daf da Zai Bar Mulkin Najeriya, Buhari Ya Amince a Kafa Sabuwar Jami'ar Tarayya

Daf da Zai Bar Mulkin Najeriya, Buhari Ya Amince a Kafa Sabuwar Jami'ar Tarayya

  • Mataimakin shugaban majalisar dattawa ya ji dadin amincewa da gina jami’ar tarayya a Kwale
  • Sanata Ovie Omo-Agege ya fitar da jawabi ta bakin Sunday Areh, yana godewa Shugaban kasa
  • ‘Dan siyasar ya yi wa mutanensa alkawari a lokacin zabe gwamnati za ta gina masu makaranta

Abuja - Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ovie Omo-Agege, ya yabi Muhammadu Buhari saboda jami’a da aka samu a jiharsa.

Gwamnatin tarayya ta amince a kafa jami’ar kiwon lafiya ta tarayya a garin Kwale a Delta, wannan abin ya yi wa Sanata Ovie Omo-Agege dadi.

Premium Times ta ce Sanata Ovie Omo-Agege ya fitar da jawabi ta bakin Sakataren yada labaransa, yana mai yabawa kokarin shugaban kasa.

Tarayya
Taron FEC na karshe Hoto: @BuhariSallauOnline
Asali: Facebook

A jawabin Sunny Areh, an ji Mataimakin shugaban majalisar dattawa yana cewa sabuwar jami’ar za ta taimakawa mutanen kasar Ndokwa.

Kara karanta wannan

"Allah Ne Ya Cece Mu" Gwamna Arewa Ya Tona Ainihin Dalilin Da Yasa Gwamnoni Suka Goyi Bayan Tinubu

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mista Sunny Areh ya ce maganar ta tabbata ne a sakamakon zama da mai gidansa ya rika yi da Ministan ilmi, har shugaban kasa ya amince.

Kyawun alkawari cikawa

Sun ta ce Omo-Agege ya yi wa al’ummma alkawari za a kafa masu wannan jami’a a yankinsu. Jihar ta na da jami'o'i uku; PTI da kuma FUPRE.

"Bayan dadewa ana muhimman tattaunawa tsakanin Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sen. Ovie Omo-Agege da Ministan ilmi, Malam Adamu Adamu da kuma umarni daga Mai girma shugaban kasa, Muhammadu Buhari, yanzu gwamnatin tarayya ta amince a kafa jami’ar kiwon lafiya ta tarayya a Kwale."
Wannan babban alheri ne ga duka mutanenmu, musamman al’ummar Ndokwa. Babban alkawari ne da aka yi lokacin yakin neman zaben da ya wuce da mataimakin shugaban kasa majalisar dattawa ya cikawa mutanen Ndokwa. Mu na masu mika duka godiya ga Ubangiji.

Kara karanta wannan

Barazanar Sanatocin Jihohin Arewa Ya Jawo APC Ta Ji Uwar Bari a Kan Takarar Majalisa

Delta ta cigaba

A jawabinsa, Sanatan na Arewacin Delta ya godewa shugaba Buhari da ya nuna kishin kasa da adalci, ya samar da makarantar nan da ake bukata.

Omo Agege yake cewa an cin ma wannan nasara ne a lokacin da mutanen yankin Ughelli za su samu babbar makarantar koyon aiki a garin Orogun.

Bola Tinubu zai karbi ragama.

Ana da labari Hadiman Muhammadu Buhari sun ce za a yabi aikin da gwamnatin nan tayi a fannin tituna, harkar noma da inganta sha'anin tsaro.

A ayyukan da aka lissafo har da ilmi, kiwon lafiya da bunkasa tattalin arziki. Muhammadu Buhari ya fara ban-kwana bayan shekaru takwas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng