Matan Zamani: Mata Ta Sace ’Yar Cikinta, Ta Nemi Kudin Fansa N3m Daga Wurin Mjinta

Matan Zamani: Mata Ta Sace ’Yar Cikinta, Ta Nemi Kudin Fansa N3m Daga Wurin Mjinta

  • Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wata mata da ake zargin ta yi garkuwa da ‘yarta a jihar
  • Matar, Rahama Sulaiman ta sace yarinyar ne ta kai ta Madobi don a ajiye ta a wurin ‘yar uwarta
  • A karshe ma’auratan sun daidaita tsakaninsu inda mijin ya tabbatar wa mutane cewa sun shirya

Jihar Kano - Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wata mata da ake zargin ta yi garkuwa da ‘yarta ‘yar shekara shida da neman kudin fansa har N3m daga mijinta.

Matar mai suna Rahama Sulaiman ta sace ‘yarta ne mai suna Hafsat Kabiru ta kai ta gidan ‘yar uwarta a Madobi ta ba a ajiyar yarinyar da nufin cewa zata yi tafiya ta kwana hudu, jaridar Daily Trust ta tattaro.

Kara karanta wannan

An Shiga Jimami Da Zubar Hawaye Yayin Da Tsageru Suka Kashe Aminin Tinubu a Imo

Police
'Yan sanda, Hoto: Daily Post
Asali: Depositphotos

Da yake karin haske, kwamishinan ‘yan sandan jihar, Muhammad Sani Gumel ya ce sun samu rahoton wannan ta’asa daga mijin matar ne Kabiru Shehu inda ya tabbatar musu cewa anyi garkuwa da ‘yar tasa.

A cewar kwamishinan 'yan sandan:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Bayan tsananta bincike, mun ceto yarinyar da akayi garkuwa da ita a karamar hukumar Madobi, matar wadda mijin nata tuni ya sake ta, ta tabbatar da cewa ita ce ta yi garkuwa da ‘yar tasu."

Wadda ake zargin ta magantu

Wadda ake zargin ta tabbatarwa ‘yan jarida cewa, mijin nata baya ba ta kudin da za ta ciyar da ‘ya’yanta kusan shekara kenan, shi yasa ta yanke shawarin yin hakan don ta ci gaba da daukan nauyin yaranta.

A kalamanta:

“Na kira shi na fada masa cewa ‘yarmu ta bata, muka tafi ofishin ‘yan sanda tare muka basu rahoto, a cikin ofishin na bashi lambar wanda zai karbi kudin fansar."

Kara karanta wannan

Mata Ta Sumar Da Mijinta Bayan Ta Lakada Masa Duka a Jihar Lagos

A karshe ta ce tayi danasanin aikata wannan mummunan laifi kuma ta tabbatar cewa sun daidaita tsakaninta da mijinta.

Rahotanni sun ce Mijin shima ya tabbatar da daidaitawar tasu, ya ce matar bata taba aikata irin haka ba.

Matasa 2 Da Suka Ci Kwalan Limamin Masallaci Sun Gamu Da Fushin Kotu

A wani labarin, Kotun shari’ar Musulunci a cikin jihar Kano ta tasa keyar wasu mutane biyu bisa zargin duka dutuncin wani limamin masallaci .

Matasan biyu, sun yi kokarin dukan limamin ne mai suna Mallam Muhammada Auwal wanda ya kasance jagora a wannan masallacin wadda su kuma suka ce basa son limancinsa a masallacin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.