Miyagun Yan Bindiga Sun Yi Ajalin Dan Siyasa da Dansa a Jihar Filato

Miyagun Yan Bindiga Sun Yi Ajalin Dan Siyasa da Dansa a Jihar Filato

  • Yan bindiga sun halaka wani ɗan siyasa da ya taba neman mukami a yankin karamar hukumar Mangu, jihar Filato
  • Mazauna kauyen sun bayyana cewa maharan sun kuma kashe ɗan mutumin kana suka jikkata matarsa wacce ke kwance a Asibiti
  • Ɗan majalisar jiha mai wakilntar Mangu ta Kudu ya tabbatar da faruwar lamarin da cewa abun babu daɗi

Plateau - Wasu miyagun 'yan bindiga sun kai hari kauyen Bureh da ke yankin ƙaramar hukumar Mangu a jihar Filato, Arewa ta Tsakiya, sun kashe mutum biyu.

Mazauna kauyen sun shaida wa jaridar Punch a Jos, babban birnin jihar ranar Alhamis cewa waɗanda maharan suka kashe sun haɗa fitaccen ɗan siyasa da ke neman muƙami, ana kiransa da John Mai Kyau da ɗansa.

Harin yan bindiga a Filato.
Miyagun Yan Bindiga Sun Yi Ajalin Dan Siyasa da Dansa a Jihar Filato Hoto: punchng
Asali: Twitter

An tattaro cewa lokacin da 'yan bindiga suka shiga kauyen da daren ranar Laraba, sun raunta matar marigayi Mai Kyau kuma tuni aka garzaya da ita Asibiti a garin Mangu.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: 'Yan Bindiga Sun Kai Sabon Hari 'Hostel' Ɗin Ɗalibai Mata a Jami'ar Arewa

Wani mazaunin garin Bureh, Salisu Maikuɗi, wanda ya tabbatar da kai harin ya ce 'yan uwa da abokan arziƙi sun yi wa mamatan janaza da yammacin ranar Alhamis.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A kalamansa ya ce:

"A daren jiya da ya wuce, 'yan bindiga sun kawo hari kauyenmu Bureh a yankin gundumar Mangu Halle, inda suka kashe mutum biyu."
"Daga cikin waɗanda aka kashe harda, John Mai Kyau, wanda ya nemi takarar wakiltar gundumarmu a matakin ƙaramar hukuma kwanakin baya."
Maharan sun kuma kashe ɗansa sun jikkata matarsa, tana kwance a Asibiti ana mata magani. Da yammacin nan muka yi wa mutanen biyu da aka kashe yayin harin jana'iza."

Ɗan majalisar yankin ya magantu kan harin

Ɗan majalisa mai wakiltar Mangu ta kudu a majalisar dokokin jihar Filato, Bala Fwangji, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce harin babban abun takaici ne, Within Nigeria ta tattaro.

Kara karanta wannan

Jiga-Jigan 'Yan Majalisa 5 Na APC Da Suka Lashi Takobin Yaƙar Ɗan Takarar Tinubu a Majalisa Ta 10

Ya ce:

"Ina Abuja yanzu amma mutane na sun kira ni sun faɗa min harin wanda ya ci rayukan mutum biyu. Idan na dawo zan je ta'aziyya ƙauyen da lamarin ya faru, abun babu daɗi."

Babu labari daga bakin yan sanda

Duk wani kokarin jin ta bakin hukumar yan san Filato ta hannun jami'in hulɗa da jama'a, DSP Alabo Alfred, bai kai ga nasara ba domin bai ɗaga kiran waya ba har kawo yanzu.

Yan Bindiga Sun Kai Hari 'Hostel' Ɗin Dalibai Mata

A wani labarin kuma Yan Bindiga Sun Kai Hari Gidan Kwanan Dalibai Mata a Jami'ar Jihar Filato

Hukumar jami'ar jihar Filato ta tabbatar da kai harin yunkurin sace ɗalibanta mata a dakunan kwanansu amma maharan ba su samu nasara ba.

A cewar jami'in hulɗa da jama'a na makarantar, jami'an tsaron jami'a ne suka fatattaki yan bindigan ba tare da sun ɗauki ko mutum ɗaya ba.

Kara karanta wannan

Akwai Matsala: Jigon Jam'iyyar APC Ya Bayyana Abu 1 Da Ka Iya Kawo Cikas Ga Rantsar Da Tinubu

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262