Ban Yi Nadama Ba: Mutumin Da Ya Taka Daga Gombe Zuwa Abuja Domin Buhari Ya Ce Zai Maimaita Idan Ya Samu Dama

Ban Yi Nadama Ba: Mutumin Da Ya Taka Daga Gombe Zuwa Abuja Domin Buhari Ya Ce Zai Maimaita Idan Ya Samu Dama

  • Dahiru Buba ya ce shi fa ko kaɗan be yi nadamar tattakin da ya yi ba a 2015, don taya Buhari murnar lashe zaɓe
  • Ya ce ko yanzu idan ya samu dama, a shirye ya ke ya sake maimaita tattakin daga Gombe zuwa Abuja domin Shugaba Buhari
  • Ya kuma roƙi duk wanda ya ke ganin ba a yi masa daidai ba a gwamnatin ta Buhari, da ya yi haƙuri ya yafe ma shugaban ƙasar

Jihar Gombe - Dahiru Buba, ɗan shekara 53, ya ce ko kaɗan be yi danasanin tattakin da ya kwashe kwanaki 15 ya na yi daga Gombe zuwa Abuja ba domin taya Buhari murnar lashe zaɓe a 2015.

Buba ya faɗi hakan ne a yayin da ya ke zantawa da kamfanin dillancin labarai na ƙasa, NAN ranar talata a garin Gombe, inda ya bayyana cewa Buhari ya cikawa 'yan Najeriya gurikansu a shekaru takwas da ya yi yana mulki.

Kara karanta wannan

Karfin Hali: Tsohon Dan Dambe Ya Tuna Baya, Ya Mangare Matarsa a Kan 'Remote' Din TV

Dahiru Buba
Dahiru Buba. Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Buhari ya yi iya bakin kokarinsa

Ya bayyana Buhari a matsayin shugaba na gari, wanda ya yi iya bakin ƙoƙarinsa wajen yin ayyukan da suka dace saboda soyayyarsa ga ƙasar tasa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ƙara da cewar gwamnatin Buhari ta yi ƙoƙari sosai, musamman ma wajen yaƙar 'yan ta'addan Boko Haram, waɗanda suka kusa amshe ƙaramar hukumarsa ta Dukku da ke jihar ta Gombe.

Ɗahiru ya ƙara da cewar irin zaman lafiyar da al'ummar yankunan da matsalar Boko Haram ta shafa a baya suke samu a yanzu, ba za ta iya misaltuwa ba kamar yadda Vanguard ta yi rahoto.

Ban yi tattaki a banza ba

Ya kuma bayyana cewa, idan ya tuno da batun tattakin kwana 15 da ya yi daga Abuja zuwa Gombe a shekarar 2015, ya na ji a ransa cewa bai yi tattakin a banza ba.

Kara karanta wannan

Akwai Matsala: Jigon Jam'iyyar APC Ya Bayyana Abu 1 Da Ka Iya Kawo Cikas Ga Rantsar Da Tinubu

Ya ce:

“Ko a yanzu in da ace zan samu dama, to zan iya maimaita tattakin saboda shugaban ƙasar.”

Dangane da masu sukar gwamnatin ta Buhari, Buba ya ce ai dama ba dole ba ne shugaban ƙasar ya iya yi wa kowane ɗan Najeriya duk abinda ya ke so.

Ya ƙara da cewa duk wanda ya ke ganin Buhari ya saɓa masa, to ya yi haƙuri ya yafe masa.

Daga ƙarshe, Dahiru ya taya gwamnan jihar Gombe Inuwa Yahaya murnar nasarar lashe zaɓen gwamna da ya ƙara yi a zaɓen da ya gabata.

Ya kuma godewa gwaman, saboda kyautar mota da kuma kuɗaɗe da ya yi masa a shekarar 2020 saboda tattakin da ya yi wa Buhari.

A shekarar 2020, Channels TV ta yi rahoto kan kyautar motar da gwamnan jihar ta Gombe Inuwa Yahaya ya bawa Dahiru Buba, da kuma wasu kuɗaɗe a dalilin wannan tattaki da ya yi.

Kara karanta wannan

Akwai Matsala: Malamin Addini Ya Hango Gagarumar Matsala a Kawancen Tinubu Da Gwamnan PDP

Zan yi tattaki don zuwa rantsar da Tinubu

A wani labarin makamancin wannan, wani matashi ya sha alwashin yin tattaki daga jihar Benue zuwa Abuja domin zababben shugaban kasa Bola Tinubu.

Matashin mai suna David Aper Nyor, ya bayyana aniyarsa ta yin tattaki daga Makurdi babban birnin jahar ta Benue domin shaida rantsar da Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng