Mummunan Karshe: Jami’an ’Yan Sanda Sun Sheke Wasu ’Yan Bindiga Har Lahira a Fitaciyyar Jihar Kudu
- Rundunar ‘yan sandan jihar Anambra ta yi nasarar kwamushe wasu ‘yan bindiga da suka addabi mutane
- Kakakin rundunar ce ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata 9 ga watan Mayu
- Ya ce anyi nasarar kashesu ne bayan sun samu bayanan sirri daga wasu mazauna yankin masu kishin kasa
Jihar Anambra - Rundunar ‘yan sandan jihar Anambra a Kudu maso Gabashin Najeriya ta ce jami’anta sun yi nasarar bindige ‘yan bindiga 2 a ranar Litinin 8 ga watan Mayu.
Kakakin rundunar a jihar, Tochukwu Ikenga ne ya tabbatar da haka a wata sanarwa da ya fitar a yau Talata 9 ga watan Mayu.
Najeriya dai na fama da hare-haren 'yan bindiga a fadin kasar musamman a Arewa maso Yamma inda 'yan bindigan ke cin karensu ba babbaka.
Mista Ikenga, ya ce an kashe ‘yan bindigan ne a yayin da jami’ansu suka fita ran gadi na hadin guiwa da ‘yan sa kai na Vigilante, jaridar Premium Times ta tattaro.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kakakin rundunar ya yi magana
Rahotanni sun tabbatar da cewa Kakakin ya fadi lokacin da wannan lamari ya faru , inda yace abun ya faru ne da misalin karfe 8:45 na dare a kan hanyar Umusiome Nkpor a karamar hukumar Idemili ta jihar.
Ya ce jami’an nasu sun samu bayanan sirri ne daga mazauna yankin akan ayyukan da ‘yan ta’addan ke yi.
“Jami’anmu sunyi artabu da ‘yan bindigan, amma munyi nasarar kashe 2 yayin da wasu 2 daga cikinsu suka tsere.”
Ikenga ya ce jami’an ‘yan sanda yanzu haka suna ta kokarin ganin sun kamo sauran ‘yan bindigan da suka tsere, don dawo dasu komar ‘yan sandan.
"Munyi nasarar kwace bindiga kirar AK-47 da alburusai da dama da wasu layu daga wurin ‘yan bindigan”
Jami'an Yan Sanda Sun Sheke Kasurgumin Dan Bindiga a Jihar Kaduna
A wani labarin, Rundunar 'yan sanda a jihar Kaduna ta yi nasarar bindige wani kasurgumin dan bindiga da ya addabi mutanen yankin bayan da suka sami bayanan sirri kan ayyukansu daga mazauna yankin.
Jami'an 'yan sandan bayan hallaka dan bindiga sun tabbatar da nasarar kwace babur din da 'yan bindigan ke amfani dasu don samun saukin zirga-zirga.
Asali: Legit.ng