Tashin Hankali Yayin da Wani Jirgin Sama Ya Yi Saukar Gaggawa a Abuja, Tayunsa Sun Kama da Wuta Nan Take

Tashin Hankali Yayin da Wani Jirgin Sama Ya Yi Saukar Gaggawa a Abuja, Tayunsa Sun Kama da Wuta Nan Take

  • Jirgin fasinja na Max Air ya yi saukar tsaiko a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke babban birnin tarayya Abuja a ranar Lahadi
  • An ruwaito cewa, jirgin ya taso ne daga Yola a jihar Adamawa da ke Arewa maso Gabas, inda tayunsa suka kama da wuta
  • Mike Ogirima, tsohon shugaban kungiyar likitoci ta NMA ya bayyana yadda hadarin ya so aukuwa sadda yake zantawa da manema labarai

An shiga tashin hankali a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja yayin da wani jirgin saman kamfanin Max Air ya yi hatsari ya sauka bayan da tayunsa suka kama da wuta a ranar Lahadi, 7 ga watan Mayu.

A cewar rahoton jaridar Daily Trust, jirgin ya fito ne daga Yola, babban birnin jihar Adamawa da ke Arewa masi Gabashin Najeriya a lokacin da lamarin ya faru.

Kara karanta wannan

Binciken masana: Yin wayan sama da mintuna 30 a mako na na mutum ya kamu da hawan jini

Nan take aka kashe wutar da ta kaman biyo bayan daukar matakin gaggawa na hukumar ceto da kashe gobara ta ARFFS da ke aiki a filin jirgin ta yi.

Yadda jirgi ya so faduwa a Abuja
Filin jirgin saman Abuja | FAAN
Asali: Facebook

Tayun sun kama da wuta ne jim kadan bayan tashin jirgin a filin tashi da saukar jiragen sama na Yola, kamar yadda Mike Ogirima, tsohon shugaban kungiyar likitocin Najeriya (NMA), ya bayyana yadda lamarin ya faru.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Bayani daga bakin tsohon shugaban NMA

Da yake bayyana yadda lamarin ya faru, ya ce:

"Allah ya taimake mu saboda mun ga yadda tayar jirgin ta fita tun daga filin sauka da tashin jirage na Yola, sai kawai muka kama addu'a.
"Ban yi magana ba a matsayina na likita saboda kada a samu firgici, amma Allah ya taimake mu."

An kwashe fasinjoji

A halin da ake ciki, an yi nasarar tattare dukkan fasinjojin da ke cikin jirgin cikin koshin lafiya, inda aka dakatar da komai har sai an gama sauke fasinjojin.

Kara karanta wannan

Ekweremadu: Abu 5 Game Da Tsohon Mataimakin Majalisar Dattawar Najeriya Da Aka Yanke Wa Shekara 10 a Birtaniya

Wani ma'aikacin kamfanin jirgin saman ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda yace an yi nasarar kwashe dukkan fasinjojin.

Ba wannan ne karon farko ba, ana yawan samun hadurran jiragen sama a Najeriya saboda wasu dalilin da ke alaka da bacin inji ko dai abu makamancin haka.

Ana yawan alakanta hakan da bacin inji ko dai wani abu daga jikin jiragen da ke daukar fasinjoji a kasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.