“Haka Nake Fama Duk Dare”: Uba Ya Goya Jinjiri Da Tsakar Dare, Ya Fadi Wahalar Da Yake Sha
- Bidiyon wani uba goye da dan karamin jariri ya yadu a dandalin sadarwa na TikTok
- Mutumin dai ya goya jinjirin ne da tsakar dare kuma yanayinsa ya nuna alamun gajiya amma babu halin hutawa
- Jinjirin wanda ke baccinsa hankali kwance ya gwammaci mahaifinsa ya kasance a cikin wannan hali yayin da shi kuma yake hutawarsa
Wani mutumi ya bayyana wasu daga cikin abubuwan da ke hawa kan namiji da zaran ya zama uba wanda ba kasafai ake fallasa su ba.
Mutumin ya nuna yadda yake goya jinjirin da misalin karfe 1:00 na tsakar dare yayin da kowa ke bacci don huta gajiya.
Bidiyon ya nuno matashin duk a gajiye sannan cewa yana matukar bukatar bacci shima abba babu yadda ya iya saboda yaron na so ya dunga jijjiga shi kafin ya iya bacci.
Yanayin mutumin sun nuna cewa sam bai san haka rayuwar zata kasance masa ba idan ya fara tara iyali.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Masu amfani da soshiyal midiya da dama da suka kalli labarin sun jinjinawa mutumin sannan sun tuna yadda nasu rayuwar ta kasance a lokacin da suka fara haihuwa suma.
Kalli bidiyon a kasa:
Jama'a sun yi martani
@Ahhh88 ta ce:
"Wasu lokutan sai ka yi ta mamakin dalilin da yasa basa bacci."
@adwoabenylwaa ta rubuta:
"Kun ga yadda abun yake da ciwo."
@BARON ya yi martani:
"Kawai ka yi hakuri...kafin ka sani, komai ya chanja kuma za ka yi kewan wannan lamari da ke bibiyarka na taba kasancewa a wannan hali da kake ciki."
@Cyndy ta yi martani:
"Kai mutumin kirki ne wasu mazan basa yi."
@user758588584:
"Nagode Allah na wuce wannan matakin yana da tsananin ciwo."
“Ba Zan Iya Bacci Ni Kadai Ba”: Uwa Ta Bude Kofar Daki, Ta Gano Diyarta Kwance a Gadon Kaninta, Mutane Sun Bata Shawara
@user7622272873975:
"Haka nake duk dare."
@Ablgall:
"Wannan karar komai ne. Dalilin da yasa ba zan sake yin ciki ba zaman daren nan yana karar da mutum."
Budurwa ta yi barazanar rabuwa da saurayinta saboda bai bata N400k ba
A wani labari na daban, wata matashiyar budurwa ta yi wa saurayinta wankin babban bargo saboda ta nemi ya turo mata kudi sai ya aika mata da N70,000.
Budurwar ta ce lallai N400k take so ya bata idan ba haka ba za ta rabu da shi.
Asali: Legit.ng