Fitacciyar Kasuwar Kasa da Kasa a Najeriya Ta Kama da Wuta
- Fitacciyar kasuwa ta ƙasa da kasa da ke karamar hukumar Ojo a jihar Legas ta kama da wuta ranar Jumu'a 5 ga watan Mayu
- Abun mamaki shi ne yadda matasa a kasuwar suka kori kungiyoyin kashe wuta da suka kai ɗauki
- Hukumar kashe gobara da ayyukan ceto ta jihar Legas ta ce jami'anta da haɗin guiwar wasu hukumomin tsaro sun fara aikin shawo kan lamarin
Lagos - Shahararriyar kasuwa ta ƙasa da ƙasa da ke jihar Legas, 'Alaba International Market' da ke Ojo, ta kama da wuta yanzu haka yau Jumu'a.
Hukumar kashe gobara da harkokin jin ƙai ta jihar Legas, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce yanzu haka jami'anta sun dira wurin domin kokarin shawo kan wutar.
Rahotanni sun nuna cewa wasu yan kasuwa sun yi uya bakin kokarinsu wajen taimaka wa kansu don kashe wutar gabanin jami'an kashe gobara su ƙariso.
Yanzu-Yanzu: Kotun Birtaniya Ta Yanke Wa Ekweremadu Shekaru 10 A Gidan Yari Kan Safarar Sassan Jikin Bil Adama
Daily Trust ta tattaro cewa a wani rahoton halin da ake ciki, Daraktan hukumar, Margaret Adeseye, ta ce:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"Rahoton da ya shigo hannun hukumar kashe gobara da ayyukan ceto ya nuna cewa wasu rumfuna a fitacciyar kasuwar ƙasa da ƙasa da ke Ojo, jihar Legas sun kama da wuta."
"A halin yanzun wasu fustattun matasa sun kori kungiyoyin kashe wuta daga Ojo, Sari-Iganmu da kuma Ajegunle, sun hana su gudanar da aikinsu amma suna nan a shirye."
"Jami'an hukumarmu da haɗin guiwar wasu hukumomin tsaro yanzu haka suna kokarin shawo kan wutar da ke ci."
Daraktan ta ƙara da cewa lamarin ya so sauya kama zuwa abinda ya shafi tsaro domin jami'an hukumar kashe wuta ba su samu ikon shiga kasuwar don gudanar da aikinsu ba a karon farko.
Adeseye ta ce hukumar ta haɗa kai da hukumomin tsaro domin shawo kan yanayin, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Gobara Ta Tashi A Ofishin Hukumar EFCC
A wani labarin mai kama da wannan, Gobara ta tashi a ofishin hukumar yaƙi da masu yi tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa (EFCC)
Lamarin dai ya faru da misalin karfe 12:30 na tsakar dare kuma ya taba wasu daga cikin gine-ginen ofishin hukumar EFCC.
Asali: Legit.ng