An Nada Sarki Ado Bayero Na Kano Shugaban Wata Babban Jami'ar Najeriya

An Nada Sarki Ado Bayero Na Kano Shugaban Wata Babban Jami'ar Najeriya

  • An nada sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero a matsayin shugaban jami’ar Calabar da ke jihar Kuros Riba
  • Gwamnatin tarayya a baya ta nada sarkin Kano a matsayin shugaban jami’ar bayan duba kwarewarsa a wannan fannin
  • Alhaji Ado Bayero ya godewa shugaba Buhari da hukumar makarantar na wannan dama da ya samu, in da yayi alkawarin kawo sauyi.

Jihar Kuros Riba - An tabbatar da sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero a matsayin shugaban jami’ar Calabar bayan da gwamnatin tarayya ta nada shi a kawanakin baya.

An nada sarkin ne a wani kasaitaccen biki da aka gudanar dakin na jami’ar da ke Calabar jiya Alhamis 4 ga watan Mayu.

Mataimakiyar shugaban jami’ar, Farfesa Florence Obi ta bayyan sarkin Kano a matsayin mutum mai kamala da kan kan da kai, jaridar The Nation ta tattaro.

Kara karanta wannan

Daga Karshe, PDP Ta Gudanar da Zabe, Ta Sanar da Sabon Shugaban Jam'iyya da Sakatare a Jiha 1

ado bayero
Sarki Ado Bayero Na Kano, Hoto: Pulse
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Ni Farfesa Obi, mataimakayar shugaban jami’ar Calabar, ina amfani da wannan dama in tabbatar da Akhaji Aminu Ado Bayero a matsayin shugaban wannan jami’a na shida, ina mai tabbatar maka da goyon bayanmu dari bisa dari, in ji Farfesa Obi.

Rahotanni sun tattaro cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya samu wakilcin shugaban ma’aikatansa Farfesa Ibrahim Gambari in da ya gabatar da kayan aiki don gudanar da ayyukansa.

Jawabin shugaba Buhari ta bakin wakilinsa Farfesa Ibrahim Gambari

“Ni shugaba Buhari,a matsayi na na wanda doka ta bani dama ina mai tabbatar da kai a matsayin shugaban wannan jami’a na 6.

“Sannan ina taya ka murna, na tabbata za ka gudanar da ayyukanka cikin tsanaki da tsoron Allah”, in ji shi.

Martani daga Sarkin Kano, Ado Bayero

Da yake jawabi, sarkin Kano Ado Bayero ya nuna farin cikin sa bisa wannan dama da godewa shugaba Buhari bisa wannan nadi da aka masa.

Kara karanta wannan

Tsohon Gwamnan Zamfara Ya Samu Goyon Bayan Na Kusa da Shugaba Buhari a Zaben Majalisa

Ya ce “Zanyi kokarin wurin tabbatar da samar da matsalolin wuraren kwana na ma’aikata da dalibai na wannan jami’a daba da yadda ake samun tururuwan jama’a zuwa nan, zan kuma tuntubi gwamnatin tarayya da sauran matsu ruwa da tsaki.
“Zamu sake duba yiyuwar sake gina dakin taro na majalisar zartaswa na wannan makaranta, a karshe ina godiya ga wannan dama da aka bani, zamu hada karfi da karfe wurin kawo cigaba a wannan makaranta”, in ji shi.

Tinubu ya Gana da Sarkin Kano da Kuma Gwamnonin APC

A wani labarin, Shugaban ƙasa mai jiran gado, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya gana da gwamnonin jam'iyyarsa ta APC a gidan da aka ware masa a birnin tarayya Abuja.

Wannan gana wa da manyan kusoshin jam'iyya mai mulki ta zo ne kwanaki kaɗan bayan zababben shugaban kasan ya dawo gida Najeriya daga Faransa, inda ya shafe kusan wata guda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.