Bayan Kwashe Kwanaki a Hannun 'Yan Sanda, An Bayar Da Belin Yunusa-Ari

Bayan Kwashe Kwanaki a Hannun 'Yan Sanda, An Bayar Da Belin Yunusa-Ari

  • Dakataccen kwamishinan zaɓe na hukumar INEC a jihar Adamawa, Farfesa Hudu Yunusa-Ari, ya samu beli
  • Hudu da shi da sauran wasu jami'ai da ke amsa tambayoyi a hannun ƴan sanda ne dai aka ba da belin su
  • Kwamishinan yana fusƙantar tuhuma ne kan zargin karɓar cin hanci lokacin zaɓen cike gurbin gwamnan jihar Adamawa

Abuja - An bayar da belin kwamishinan zaɓen hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) na jihar Adamawa wanda aka dakatar, Farfesa Hudu Yunusa-Ari, rahoton The Nation ya tabbatar.

Haka kuma sauran mutum biyun da aka yar je mu su samun beli, su ne wasu kwamishinoni na ƙasa mutum biyu na hukumar INEC, da sauran wasu jami'ai waɗanda ke amsa tambayoyi a hedikwatar rundunar ƴan sanda ta ƙasa, kan rikita-rikitar da ta faru a zaɓen gwamnan jihar Adamawa.

Kara karanta wannan

Faragaba Ta Ƙaru, Hukumar Sojin Najeriya Ta Fallasa Masu Hannu a Shirin Hana Rantsar da Bola Tinubu

An bayar da belin Yunusa-Ari
Dakataccen kwamishinan INEC na jihar Adamawa, Farfesa Hudu Yunusa-Ari Hoto: Thenation.com
Asali: UGC

An dai sake su ne a kan beli, wanda ya zo da sharuɗɗa. sharuɗɗan belin na su, sun haɗa da:

  • Dole ne su ajiye fasfo ɗin su na tafiya
  • Ba za su fita wajen babban birnin tarayya Abuja ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

An samo cewa wani sanata ne ya tsayawa Hudu-Ari, bayan ya kwashe kwana uku yana amsa tambayoyi yayin da ya ke tsare a hannun ƴan sanda.

Babban sufeton ƴan sanda na ƙasa, Alkali Usman Baba, shi ma sai da ya yi wa Hudu-Ari da sauran waɗanda su ke tsare tare tambayoyi. A tare da IGP lokacin tambayoyin akwai mataimakan babban sufeto (DIG), cewar rahoton Daily Trust.

Majiyoyi sun bayyana cewa Yunusa-Ari, ya yi musanyar kalamai da kwamishinonin hukumar INEC na ƙasa, kan cewa ya tsere ya yi ɓatan dabo.

An dai yi mu su tambayoyi ne kan zargin karɓar na goro a lokacin zaɓen cike gurbi na gwamnan jihar Adamawa a ranar 15 ga watan Afirilu, wanda Hudu ya bayyana ƴar takarar jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Aishatu Dahiru Binani, a matsayin wacce ta yi nasara ana cikin tattara sakamakon zaɓe.

Kara karanta wannan

Tashin Hankalin Da Muka Shiga a Sudan Ba Ɗan Kaɗan Ba Ne, In Ji Ɗalibi Bello Halliru

Kwamishinan Zaben Adamawa Bai Yi Dana Sanin Ayyana Binani Ba

A baya rahoto ya zo kan yadda Hudu Yunusa-Ari, ya bayyana cewa bai yi dana sanin bayyana ƴar takarar jam'iyar APC, a matsayin wacce ta lashe zaɓen gwamnan jihar Adamawa ba.

Hudu ya dai bayyana Aishatu Dahiru Binani a matsayin wacce ta lashe zaɓen, ana cikin tattara sakamakon zaɓe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng