Karshen Duniya: Matashi Ya Daba Wa Mahaifiyarsa Wuka Har Lahira a Kano
- Wani matashin ɗan Saurayi ya burma wa mahaifiyarsa wuƙa har lahira a jihar Kano ranar Laraba da yamma
- Ganau ya ce sun gaggauta kai matar mai suna Jummai Asibiti amma Likita ya tabbatar da rai ya yi halinsa
- Kakakin hukumar 'yan sandan jihar Kano, Abdullahi Kiyawa, ya ce nan da ba jimawa ba zai fitar da cikakken bayani
Kano: Wani abun tashin hankali ya auku da yammacin Laraba a Karshen Kwalta, rukunin gidajen Rimin Kebe da ke ƙaramar hukumar Ungoggo a jihar Kano.
Punch ta rahoto cewa wani matashin yaro mai suna, Iro Kwarangwal, ya caka wa mahaifiyarsa da ta duƙa ta haife shi, Jummai, wuƙa har lahira, lamarin ya ta da hankalin mutane.
Lamarin ya faru a wannan rana da ta zama baƙa ga mazauna Anguwar da misalin ƙarfe 5:30 na yamma.
Yadda abun ya faru tun farko
Wani ganau, wanda ya nemi a ɓoye bayanansa ya shaida wa wakilin jaridar cewa, "Ina tsaye a ƙofar gidana, na jiyo ƙara daga gidan matar."
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya bayyana cewa yayin da ya yi saurin shiga gidan domin kai ɗauki, ya taras da matar kwance bayan soka mata wuƙa a wurare daban-daban, tana kururuwar neman taimako.
Mutumin ya ƙara da cewa wanda ake zargi ya gudu jim kaɗan bayan aikata wa mahaifiyarsa wannan ɗanyen aiki, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.
Ganau ɗin ya yi bayanin cewa nan take suka garzaya da matar zuwa Asibiti a Keke Napep jini na ta kwarara a jikinta, daga bisani likita ya tabbatar da rai ya yi halinsa.
"Tun jiya aka mata jana'iza aka kaita makwancinta kamar yadda addinin Musulunci ya tanada. Allah ya gafarta mata ya sanya ta a cikin gidan Aljanna," inji shaidan gani da iso.
Yayin da aka tuntuɓe shi, jami'in hulɗa da jama'a na rundunar yan sandan jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin kuma ya yi alkawarin sanar da cikakkrn bayani nan gaba.
Sojoji Sun Ceto Ma'aikatan Jin Kai Daga Hannun Yan Ta'adda
A wani labarin, mun kawo muku rahoton yadda Dakarun Soji Sun Ceto Ma'aikatan Jin Kai da Yan Ta'adda Suka Sace a Borno
Biyu daga cikin ma'aikatan kungiyar NGO 3 da mayakan ISWAP suka sace a jihar Borno sun shaƙi iskar yanci ranar Laraba.
Har yanzun akawai sauran mutum uku a hannun 'yan ta'addan kuma har yanzun mahukunta ba su ce uffan ba kan lamarin.
Asali: Legit.ng