An Raba Wa ’Yan Najeriyan da Aka Kwaso Daga Sudan N100k, Katin N25k da Data 1.4GB a Abuja
- Gwamnatin Najeriya ta karbi rukunin farko na ‘yan kasar da suka makale a kasar Sudan yayin da yaki ya balle a kwanakin baya
- Akalla mutum 376 ne suka sauka a filin saukar jiragen sama na kasa da kasa na Nnmadi Azikiwe da ke Abuja a ranar Laraba
- An raba wa dukkan wadanda aka kwaso daga Sudan kyautar kudi N100,000 da karin N25,000 na katin waya da 1.5GB na data
FCT, Abuja – Gwamntin tarayyar Najeriya ta karbi rukunin farko na ‘yan Najeriyan sama da 350 da suka makale a Sudan kana suka tsere Masar a ranar Laraba 3 ga watan Mayu.
A lokacin da suka sauka, gwamnatin tarayya ta raba musu kudi N100,000 kowannensu tare da kara musu N25,000 na katin waya da kuma 1.5GB na data.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa, an yi rabon kudin ne a karkashin ma’aikatar jin kai. Minista Sadiya Umar Farouk ce ta tabbatar da hakan a yau Alhamis 4 Mayu, 2023 a filin filin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.
Ta kuma tabbatar da cewa, dukkan mutum 350 da aka kwaso sun sauka a Abuja da misalin karfe 11:35 na dare, inda gwamnatin tace ana ci gaba da kokarin kwaso wasu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda aka raba kudi, daga bakin Hajiya minista
Da take bayanin yadda aka raba tallafin da kuma wadanda suka ba da kudi da katin, ministar ta ce, kamar yadda NairaMetrics ta ruwaito.
“Ina godiya ga dukkan al’ummar da suka yi kokari wajen tabbatar da wadannan mutanen sun dawo lafiya kuma a mutunce. Muna godiya ga kamfanonin sufurin bisa tallafinsu.
“Akwai kudi N100,000 da zai kai su ga ahalinsu wanda tallafi ne daga gidauniyar Dangote ta hanyar ba su kudin sufuri da kuma katin waya na 25,000 daga MTN da kuma 1.5GB data daga MTN.
“Duk wani kokari an yi shi kuma kowa ya ba da gudunmawa wajen tabbatar da akalla wadannan ‘yan Najeriyan sun samu hanyar dawowa gida lafiya.”
Za a kashe $1.2m wajen kwaso ‘yan Najeriya daga Sudan zuwa Masar
A wani labarin, kunji yadda ma’aikatar waje ta Najeriya ta bayyana adadin kudaden da za a kashe wajen kwaso ‘yan Najeriya daga Sudan zuwa Masar.
A cewar ma’aikatar, za a kashe $1.2m wajen hayar motoci bas da za su yi jigilar ‘yan kasar gabanin kwaso su zuwa Najeriya kai tsaye.
Asali: Legit.ng