Jama’a Sun Barke da Zanga-Zanga a Hedikwatar CBN, Suna Neman Emefiele Ya Yi Murabus

Jama’a Sun Barke da Zanga-Zanga a Hedikwatar CBN, Suna Neman Emefiele Ya Yi Murabus

  • ‘Yan Najeriya sun fito zanga-zanga don nuna kin jinin ci gaba da kasancewar Godwin Emefiele a kujerar gwamnan CBN
  • Sun kuma nemi gwamnan da ya tabbatar da sabbin kudi sun wadata a kasar nan ba da jimawa ba daidai da umarnin kotu
  • ‘Yan Najeriya sun shiga kunci a farkon shekarar nan tun bayan da aka bayyana batun sauya fasalin Naira daga CBN

FCT, Abuja - Rahoto ya bayyana cewa, ‘yan Najeriya da yawa sun mamaye hedkwatar Babban Bankin Najeriya (CBN) tare da neman Godwin Emefiele ya yi murabus cikin gaggawa.

Zanga-zangar an ce suna yinta game da yadda sabbin ka’idojin babban bankin kasar game da Naira ya jawo wahalhalu ga ‘yan Najeriya, rahoton Punch.

‘Yan zanga-zangar da aka ga suna yi a bakin babban bankin, an ga ‘yan Najeriya da yawa na dauke da allunan gangamin da ke nuna kin jinin ci gaba da shugabacin Emefiele.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali Yayin Da Aka Yi Wa Wasu Matasa Biyu Yankan Rago a Jihar Filato

'Yan Najeriya na neman a tsige Emefiele
Gwamnan CBN Godwin Emefiele | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Ba za mu tafi ba sai an biya mana bukata, inji masu zanga-zanga

Sun kuma yi barazanar cewa, ba za su bar hedkwatar ba har sai an amsa bukatarsu da suka gabatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu daga kalaman da aka rubuta a jikin allunan zanga-zangar sun nuna ‘Emefiele Must Go’, ‘CBN Now Bureau De Change’ da dai sauran magangancu masu nuna rashin amince da Emefiele.

Da yake zantawa da manema labarai, wanda ya hada zanga-zangar, George Uboh ya ce:

“Muna neman Godwin Emefiele a matsayinsa na gwamnan CBN da ya tabbatar wanzuwar sabbin takardun Naira.
“Kuma dole ya fito nan ya yiwa mutane jawabi saboda kotun koli a hukuncinta ta ce sabbin Naira sun ya jefa ‘yan Najeriya a cikin kunci.”

CBN ta jawo wa ‘yan Najeriya kunci

Ya kara da cewa, dokokin da CBN ta kawo sun zama tubalin kisan kare dangi ga ‘yan Najeriya, inda yace ba da bindiga kawai ake karar da al’umma ba, dokoki irin na CBN ma sun wadatar.

Kara karanta wannan

Kaico: Duk da Buhari ya ba da kudin bas $1.2m, motoci sun ki kwaso 'yan Najeriya daga Sudan

Ya kuma zargi babban bankin na Najeriya da rashin tausayin ‘yan kasar da basu ji ba basu gani ba haka siddan, Ripple Nigeria ta tattaro.

A baya kuma, CBN ya ce akwai wadatattun kudade a kasar nan, sai dai bankuna ne suka ki zuwa domin dauka su raba wa mutane.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.