An Sanar Da Ranar Da 'Yan Najeriyan Da Rikicin Sudan Ya Ritsa Da Su Za Su Dawo Najeriya

An Sanar Da Ranar Da 'Yan Najeriyan Da Rikicin Sudan Ya Ritsa Da Su Za Su Dawo Najeriya

  • Bayan kwashe kwanaki cikin halin rashin tabbas da ɗar-ɗar, yau ƴan Najeriya da suka maƙale a Sudan za su fara isowa gida
  • Ƴan Najeriyan da rikicin na Sudan ya ritsa da su, za a kwaso su ne daga ƙasar Egypt zuwa birnin tarayya Abuja
  • Shirye-shirye duk sun kammala domin jiragen da za su kwaso su sun kimtsa tsaf domin yin jigilar su zuwa gida Najeriya

Abuja - Aƙalla ƴan Najeriya da suka maƙale a Sudan, mutum 354 waɗanda aka kwaso su daga ƙasar ake sa ran isowar su, gida Najeriya a yau ranar Laraba.

Jaridar Tribune tace a bisa tsarin da aka yi, jirgin saman rundunar sojin saman Najeriya, NAF C-130 zai ɗauko mutum 80, yayin da jirgin kamfanin jirgin sama na Air Peace zai ɗauko mutum 274.

Kara karanta wannan

Ziyarar Tinubu Zuwa Rivers: Gwamna Wike Ya Ayyana Ranar Hutu a Jihar Domin Tarbar Zababben Shugaban Kasa

Yau 'yan Najeriya za su fara isowa daga Sudan
Yau ake sa ran isowar 'yan Najeriyan da suka makale a Sudan gida Najeriya Hoto: Tribune.com
Asali: UGC

Ƴan Najeriyan dai za a kwaso su ne a Aswan cikin ƙasar Egypt akan jiragen rundunar sojin saman Najeriya, (NAF C-130)da kuma jirgin kamfanin Air Peace.

Jirgin rundunar sojin saman na NAF C-130, yana a ƙasar Egypt tun ranar Lahadi, a yayin da aka tsayar da jirgin Air Peace a Najeriya har zuwa lokacin da hukumomin ƙasar Egypt za su sahale ƴan Najeriyan su shigo cikin ƙasar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Shugabar hukumar kula da ƴan Najeriya mazauna ƙasashen waje (NiDCom), Hon. Abike Dabiri-Erewa, ta tabbatar da halin da ake ciki a shafinta na Twitter.

Hon. Dabiri-Erewa, wacce tare da ministan harkokin ƙasashen waje suka tattauna da kakakin majalisar wakilai, Hon. Femi Gbajabiamila, bayan kammala zaman majalisar na ranar Talata, ta tabbatar da dukkanin ƴan Najeriyan sun isa tashar jirgin ruwan Sudan.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Motar Bas Ɗauke da Ɗaliban Najeriya 50 Daga Sudan Ta Kama da Wuta

An dai sha taƙaddama kafin Egypt ta barin ƴan Najeriyan da aka kwaso su shiga ƙasar ta, saboda dalilai na diflomasiyya.

Motar Bas Da Ta Dauko Daliban Najeriya Daga Sudan Ta Kama da Wuta

A wani rahoton na daban kuma, kun ji yadda wata motar bas ɗauke da ƴan Najeriyan da ake kwasowa daga Sudan ta kama da wuta.

Motar bas ɗin tana kan hanyar ta ne ta kai ƴan Najeriyan da ta ɗauko zuwa tashar jirgin ruwan Sudan, lokacin da lamarin ya auku.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng