Saura Kwanaki 27 Ya Sauka, Buhari Ya Tsige Shugaban HYPREP, Ya Sanar a Twitter
- Muhammadu Buhari ya sa hannu kuma ya amince a canza shugaban da ke kula da aikin HYPREP
- Shugaban Najeriya ya kawo Farfesa Nanibarini Zabbey domin maye gurbin Dr. Ferdinand Giadom
- Nanibarini Zabbey ya kware wajen binciken da suka shafi gurbacewar kasar Ogoni a Neja Delta
Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da korar Dr. Ferdinand Giadom daga matsayin da yake kai na shugaban aikin HYPREP.
Sanarwar korar Dr. Ferdinand Giadom ta fito ne ta shafin Twitter na fadar shugaban kasa, @NGRPresident a cikin farkon mako mai-ci.
An kirkiro aikin HYPREP ne domin magance matsalar gurbata Neja-Delta da sinadarai masu illa.
A yayin da aka tabbatar da tsige tsohon malamin makarantar, nan take sanarwar ta bayyana cewa an nada wani wanda zai jagoranci aikin.
An samu sabon shugaba
Farfesa Nanibarini Zabbey ne zai maye gurbin Giadom, fadar shugaban Najeriyan ta kuma ce zai fara aiki ne ba tare da wani bata lokaci ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Shugaban kasa @MBuhari ya amince da korar shugaban aikin @HYPREPNigeria, Dr. Ferdinand Giadom.
- Fadar Shugaban kasa
Tare da nadin Farfesa Nanibarini Zabbey a a matsayin sabon shugaban aikin ba tare da wani wata-wata ba.
A rahoton The Nation ne aka fahimci cewa sanarwa ta fito daga ma’aikatar muhalli ta kasa wanda ta tabbatar da cewa Giadom ya bar ofis.
Sanarwar Olusegun Shogbola
Mai magana da yawun bakin Ministan tarayya, Olusegun Shogbola ya shaida cewa an yi canjin wanda zai jagoranci wannan aiki da ake yi.
Farfesa Zabbey ya kware sosai a kana bin da ya shafi harkar sinadaran cikin ruwa, ya yi suna wajen tsabtace wurare daga sinadarai masu illa.
Kafin zamansa shugaban HYPREP, This Day ta ce Farfesan malamin makaranta ne a sashen aikin gona na jami’ar tarayya da ke Fatakwal.
Zabbey ne mutumin Afrika na farko da aka taba lambar yabo na kungiyar masana teku na ASLO, sannan an yaba da bincikensa a Neja Delta.
Zaben shugaban majalisa
An samu rahoto kusoshin da ke majalisar dattawa sun jawo wani tsohon shugaban majalisar domin a maimaita abin da ya faru a zaben 2015.
Ana tara dukiya domin Abdulaziz Yari ya karbi majalisa, ana so ya samu goyon bayan akalla Sanatoci 60 daga duka jam'iyyun da ake da su.
Asali: Legit.ng