Mata Ta Shiga Motar ’Yan Damfara, Ta Dauki Bidiyonsu Basu Sani Ba, Ta Yada a Duniya

Mata Ta Shiga Motar ’Yan Damfara, Ta Dauki Bidiyonsu Basu Sani Ba, Ta Yada a Duniya

  • Wata matar ‘yar Najeriya da ta kubuta daga damfarar ‘yan 419 ta fito a kafar sada zumunta don ba da labarin yadda abin ya faru
  • A cewarta, wannan ne karo na biyu da hakan ke faruwa da ita, inda tace ‘yan damfarar sun bi salo ne iri daya
  • Jama’ar da suka gamu da irin wannan sun bayyana abin da ya taba faruwa dasu na damfara don jajantawa matar

Wata ‘yar Najeriya mai suna Stella ta yi sa’a sau biyu yayin da ta shiga motar ‘yan damfara masu karbe ‘yan kudaden jama’a.

Bayan shiga motar, Stella ta gano cewa wadanda ke cikinta ‘yan damfara ne, sai ta dauki bidiyonsu a hankali yayin da suke magana basu sani ba.

Da ta yada bidiyon a TikTok, ta ce dukkan ‘yan 419 da ta hadu dasu sun bi salo ne iri daya kuma wannan ne karo na biyu da ta taba haduwa dasu.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali Yayin Da Aka Yi Wa Wasu Matasa Biyu Yankan Rago a Jihar Filato

Yadda mata ta tona asirin 'yan 419
'Yan 419 a lokacin da suke kokarin yin sata | Hoto: @stella_pepperish
Asali: TikTok

Stella ta kuma ce, ‘yan damafar nunawa suka yi kamar basu san juna ba a lokacin da suka dago batu kan kudi don yaudarar fasinjoji su tsoma baki a damfare su.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A bidiyon, Stella cikin dabara ta dauke su bidiyo basu sani a lokacin da suka saki baki suna ba da labarin yadda za a samu kudi.

Ta rubuta:

“Wadannan mutanen sun yi mirsisi kamar basu san juna ba kuma suke cewa wai akwai kudi a bayan mota idan ka yaudaru ta kare maka.”

Kalli bidiyon:

Martanin jama’a

Ajose_racheal:

“Irin wannan ya faru dani a kusa da otal din eko, kuma irin haka na yi, na gaggauta sauka, sai ya zuri mutarsa.”

Rotbol Boluwaji Oluwarotimi:

“Na farko na karanta irin wannan a cikin littafin hikaya a 2004, washe gari suka damfar ‘yar uwa, ni da mai gidana mun hau motarsu sau biyu a kusa da Ondo.”

Kara karanta wannan

Kaico: Duk da Buhari ya ba da kudin bas $1.2m, motoci sun ki kwaso 'yan Najeriya daga Sudan

Ewadamisola:

“Nima sun min haka ojuelegba zuwa cms suka ce suna bukatar kudi za su sauya dalarsu don haka za su sayar da wayarsu cewa za su bani.”

Awe Brightness:

“Sun yi amfani da irin wannan a kaina a jihar Ekiti...Omo! mutum 4 a kai na na gani ranan. Nagode Allah ban samu ‘ojukokoro’ ba.”

Cindeehairs:

“Kamar na san fuskokinsu ma...Ina tuna yadda irin wannan ya faru da yadda matar da aka yiwa ta fashe da kuka.”

Holayyide:

“Allah ya tsare ki gaskiya.,wannan ya faru dani kuma tuni na gane tare suke.”

Tfhairstore:

“Haka ya faru dani a Akure lokacin da nake IT a 2018 kai matar da ke zaune a kusa dani sai cewa take na zauna tare da ita domin ita ke da kudin.”

Wata kuwa rashin saurayi tayi bayan da ta ci amanarsa kan tsohon saurayinta da ba aurenta zai yi ba.

Kara karanta wannan

Garin dadi: Mata ta bar Najeriya, yadda ake siyar da daurin tuwo 1 N920 ya bata mamaki

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.