EFCC Ta Kama Daliban Jami'a 19 Bisa Zargin Damfara Ta Intanet

EFCC Ta Kama Daliban Jami'a 19 Bisa Zargin Damfara Ta Intanet

  • Jami'an hukumar EFCC sun yi ram dalibai 19 na jami'ar jihar Akwa Ibom kan tuhumar aikata laifin zamba a Intanet
  • A wata sanarwa da EFCC ta fitar ranar Talata, ta ce an kama waɗanda ake zargin ne a ɗakin kwanan ɗalibai ranar Jumu'a
  • Bayan kwace na'urori masu kwakwalwa da wayoyi a hannunsu, EFCC ta ce zata maka su a Kotu bayan gama bincike

Akwa Ibom - Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ta kama ɗalibai 19 na jami'ar jihar Akwa Ibom bisa zarginsu da aikata laifuka a Intanet.

EFCC ta bayyana haka a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Tuwita ranar Talata, ta ce ta kama waɗanda ake zargi ranar Jumu'a 28 ga watan Afrilu, 2023.

Daliban da EFCC ta kama.
EFCC Ta Kama Daliban Jami'a 19 Bisa Zargin Damfara Ta Intanet Hoto: @officialEFCC
Asali: Twitter

Hukumar ta bayyana cewa dakarunta sun damƙe ɗaliban da ke karatu a ɗakunan kwanansu da ke Ikot Akpadem a ƙaramar hukumar Mkpat-Enin, jihar Akwa Ibom.

Kara karanta wannan

To Fa: Kwamishinan Zaben Adamawa Ya Ƙara Shiga Sabon Tasku Kan Ayyana Aishatu Binani

Wane laifi ake tuhumar ɗaliban da aikatawa a Intanet?

A sanarwan da ta wallafa, EFCC ta ce:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Jami'an EFCC na reshen Uyo, babban birnin Akwa Ibom sun damƙe ɗaliban jami'a da ke karatunsu a jami'ar jihar Akwa Ibom ranar Jumu'a 28 ga watan Afrilu, 2023 bisa zargin aikata laifukan intanet."
"Mun kama daliban ne bayan watanni ana sa ido kan zargin hannunsu a damfara, mu'amalar kudaɗen intanet watau Crypto na ƙarya da kuma Sojan gona."
"Zamu gurfanar da su a gaban Kotu da zaran jami'ai sun kammala duk wani bincike kan zarge-zargen da ake musu."

Abubuwa da aka kwato a hannun ɗaliban

Hukumar EFCC ta bayyana irin abubuwan da ta kwace daga hannun ɗaliban wanda suka haɗa da na'ura mai kwakwalwa da kuma wayoyin hannu.

A wani labarin kuma Daliban Najeriya Da Motarsu Ta Kama Da Wuta Sun Isa Tashar Jirgin Ruwan Sudan

Kara karanta wannan

Nasara Daga Allah: Bayan Shakaru 9, Sojojin Najeriya Sun Ƙara Samun Babbar Nasara a Borno

Idan baku manta ba mun kawo yadda wasu yan Najeriya suka gamu da matsala a hanyarsu ta zuwar tashar jirgin ruwan Sudan, inda za'a kwaso su zuwa gida.

Akalla mutun 10 suka kwana a wurin amma tuni suka ci gaba da tafiya, zuwa yanzu an ce sun isa tashar jirgin ruwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262