Gwamnatin Buhari Ta Fara Shirye-shiryen Cefanar da Asibitin Fadar Shugaban Kasa

Gwamnatin Buhari Ta Fara Shirye-shiryen Cefanar da Asibitin Fadar Shugaban Kasa

  • Gwamnatin Muhammadu Buhari a yunkurinta na neman kudi, za ta cefanar da wasu wurare
  • Bayanai sun nuna ana kokarin ganin an saida wani asibitin fadar shugaban kasa ga ‘yan kasuwa
  • Babban Sakataren gwamnatin tarayya na fadar shugaban kasa ne ya shaida haka a wajen wani taro

Abuja - Fadar shugaban kasa ta hada-kai da ma’aikatar kudi, kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki domin a sa wasu kadarori a kasuwa.

A rahoton da mu ka samu daga Daily Trust, an fahimci gwamnatin tarayya ta gano wasu hanyoyi har uku da za a iya samun kudin shiga.

Akwai wasu tsare-tsare da ayyukan da ake tunanin za a hada-kai da ‘yan kasuwa, hakan ya na nufin za a shiga yarjejeniyar nan ta PPP.

Babban sakataren gwamnatin tarayya na fadar shugaban kasa, Tijjani Umar ya yi wannan bayani da yake magana a jiya a garin Abuja.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari Ya Fadawa Bola Tinubu Alfarmar da Yake Nema a Wajen Gwamnatinsa

An yi zaman taron 3PUPCF a Abuja

Umar ya halarci taron 3PUPCF da fadar shugaban kasa da kuma hukumar ICRC suka shirya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar shi abubuwa uku da ake tunanin damkawa ‘yan kasuwa sun hada da sashen kula da gandun daji da gidan filin wasan yara.

Fadar Shugaban Kasa
Fadar Aso Rock Villa Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Rahoto ya tabbatar da cewa akwai batun babban asibitin fadar shugaban kasa da dakin shan magani da ake da su ke garin Legas.

Kafin babban birnin tarayya ya zama Abuja a lokacin mulkin soja, Legas tayi shekara da shekaru a matsayin birnin tarayya a Najeriya.

Linda Ikeji ta fitar da labari an yi nisa wajen shirin cefanar da asibitin fadar shugaban kasar domin a ji dadin tafiyar da su da kyau.

Gyara asibitin Aso Rock

Hakan yana zuwa ne bayan gwamnatin Najeriya ta batar da akalla N8.5bn wajen gyaran asibitin da ke cikin fadar Aso Rock da ke garin Abuja.

Kara karanta wannan

Fadar Shugaban Kasa Ta Fitar da Shafuka 90 a Kan Jerin Nasarorin da Buhari Ya Samu

Kafin nan an dauki lokaci ana kukan asibitin ya tabarbare, wannan ya sa aka ware makudan biliyoyi domin a rika kula da jami’an gwamnati.

Gidan da Seyi Tinubu ya saya

Bincike ya nuna ana zargin Oluseyi Tinubu ya saye gidan Kolawole Aluko a Landan, har Muhammadu Buhari ya taba ziyartar Bola Tinubu a nan.

Tun a 2016 Hukumar EFCC ta ke binciken wanda ya mallaki gidan a badakalar Diezani Alison-Madueke, an yi cinikin ne kan Dala miliyan 10.8.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng