Fadar Shugaban Kasa Ta Fitar da Shafuka 90 a Kan Jerin Nasarorin da Buhari Ya Samu

Fadar Shugaban Kasa Ta Fitar da Shafuka 90 a Kan Jerin Nasarorin da Buhari Ya Samu

  • Fadar shugaban Najeriya ta tattaro irin manyan nasarorin da gwamnatin tarayya ta samu a Najeriya
  • Femi Adesina ya fitar da takarda kunshe da cigaba da Muhammadu Buhari ya kawo a shekaru takwas
  • Mai girma Muhammadu Buhari ya dare kan mulki a Mayun 2015, saura ‘yan kwanaki ya bar ofis

Abuja - Fadar shugaban kasa ta jero wasu daga cikin abubuwan yabawa na gwamnatin Muhammadu Buhari daga Mayun 2015 zuwa shekarar 2023.

A rahoton da Premium Times ta fitar a ranar Litinin, an ji labari Hadimin shugaban kasa, Femi Adesina ne ya tattaro nasarorin da aka samu a mulkin APC.

Hadimin shugaban kasar ya fitar da bayani mai tsawon shafuka 90 a karshen makon jiya dauke da cigaban da aka gani ta fuskar tattali, tsaro da dai sauransu.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Yari Ya Gana Da Buhari, Ya Ce Arewa Ta Cancanci Shugabancin Majalisar Dattawa

Femi Adesina ya ce daga 2016, hukumar kula da shige da fice watau NIS ta gina manyan ofisoshi 17 a fadin kasar nan, har yanzu kuma ana gina wasu hudu.

NIS ta kawo cigaba

A kan batun NIS, Adesina ya ce an kawo fasfo na komfuta da takardar fita ketare mai shafe shekaru goma baya ga ofisoshi da aka bude a wasu kasashen waje.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Fadar shugaban kasar ta ce NIS ta kirkiro fasahohi na zamani domin cafke masu laifi tare da sa ido a kan duk wanda yake shiga ko ficewa daga tashar Najeriya.

Fadar Shugaban Kasa
Shugaba Muhammadu Buhari Hoto: @BuhariSallauOnline
Asali: Facebook

NDLEA ta na kokari a yau

Rahoton ya ce a bangaren yaki da miyagun kwayoyi, hukumar NDLEA ta cafke mutane 24, 000 da ke safarar kwayoyi, kuma an daure mutane fiye da 3, 400.

A shekarun 2021 da 2022, NDLEA ta karbe kilo miliyan 5.5 na kwayoyi wanda darajarsu takai N450bn, sannan an rusa eka 772.5 na gonar wiwi a kasar nan.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Jirgin Shugaban Kasa Ya Lula Kasar Waje Domin Samun Gyara Na Musamman

The Nation ta ce Adesina yana tunkaho da yadda gwamnatin Buhari tayi wa fursunoni 2, 600 afuwa, hakan ya jawo aka rage yawan cunkoso a gidajen yari.

Yau ta fi jiya kyau?

Mai magana da yawun bakin shugaban na Najeriya ya ce idan za ayi kallon adalci, za a fahimci Muhammadu Buhari ya yi matukar kokari a kan karagar mulki.

A cewar Adesina, gwamnatinsu ba za ta bar mulki a yadda ta karba ba, an kawo gyara iri-iri.

Rikicin Gwamnatin tarayya v El-Rufai

Labari ya zo cewa a watan Afriku, ma’aikatan KASUPDA su ka shiga makarantar FGC Malali, sun ruguza bangaren katangarta, hakan ya jefa al'umma a hadari.

An samu wasu jami’an gwamnatin tarayya da suka dauki mataki a kan lamarin, za su yi shari’a da Malam Nasir El-Rufai, kuma sun ankarar da 'yan sanda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng