Hotuna Sun Bayyana Yayin Da Mai Kula Da Tsaron Lafiyar Zababben Shugaban Kasa Tinubu Ya Kama Aiki

Hotuna Sun Bayyana Yayin Da Mai Kula Da Tsaron Lafiyar Zababben Shugaban Kasa Tinubu Ya Kama Aiki

  • A shirye shiryen bikin rantsuwa ranar 29 ga Mayu, zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya zabi Laftanar Kanar Nurudeen Alowonle Yusuf a matsayin babban mai tsaronsa (ADC)
  • Yusuf, da ne ga Oba Yusuf Omokanye Oyekanmi, Elomona na Illemona da ke karamar hukumar Oyun a Jihar Kwara
  • Abin birgewa, ranar Litinin, 1 ga watan Mayu, Laftanar Yusuf ya kama aiki, a matsayin sabon mai tsaron lafiyar zababben shugaban kasa, Tinubu

Laftanar Kanar Nurudeen Alowonle Yusuf, dan basarake, Oba Yusuf Omokanye Oyekanmi, Elomona na Illemona a karamar hukumar Oyun da ke Jihar Kwara, ya kama aiki a matsayin sabon mai tsaron lafiyar zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Jaridar Daily Trust a ranar Litinin, 1 ga watan Mayu, ta ruwaito cewa Yusuf ya kama sabon aikinsa mako uku kafin bikin rantsar da shugaba mai jiran gado, karkashin jam'iyyar APC mai mulki.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Yari Ya Gana Da Buhari, Ya Ce Arewa Ta Cancanci Shugabancin Majalisar Dattawa

Mai tsaron lafiyar Tinubu
Laftant Kanal Yusuf ya kama aiki a matsayin mai tsaron lafiyar Bola Tinubu, zababben shugaban kasa. Hoto: @EleyiLagos
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sabon ADC ga Tinubu Kanar Yusuf ya kama aiki

Yariman haifaffen Kwara an ruwaito yana aiki a fadar shugaban kasa kafin nadin na shi.

Wata majiya ta ruwaito cewa sabon ADC din ya taba riki wani babban makami a lokacin mulkin tsohon shugaba Jonathan, rahoton Vanguard ma ya tabbatar da haka.

Wannan na nufin Yusuf zai yi aiki da kwarewarsa da sanin makamar aiki don gudanar da sabon aikinsa.

Buhari ya bayyana dalilin da ya sa Tinubu ya kada Atiku, Obi, da sauransu

A gefe guda, shugaba Buhari ya bayyana dalilin da ya sa Jami'yyun adawa suka sha kaye a hannun jami'yyar APC.

Buhari, a wani sako da ya fitar ya bayyana Atiku Abubakar da Peter Obi, yan takarar PDP da LP, wanda su ne manyan yan adawa, a matsayin wanda suka cika zumudi.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Buhari Ya Tsawaita Wa'adin Shugaban Hukumar Shige Da Fice

Shugaban ya bayyana lokacin zabe cewa, jam'iyyar APC na aiki tukuru don cigaba da mulki, su kuma jam'iyyun adawa suna yaudarar kansu da zumudi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164