Sojoji Sun Ceto Dalibar Makarantar Chibok Dauke da Juna Biyu

Sojoji Sun Ceto Dalibar Makarantar Chibok Dauke da Juna Biyu

  • Dakarun sojin Bataliya ta 114 sun ceto ɗalibar makarantar Chibok mai suna, Hauwa Maltha, ɗauke da juna biyu
  • Hauwa tare da ɗiyarta yar shekara uku, Fatima, sun kubuta ne lokacin da Sojoji suka kai samame Lagara a watan Afrilu
  • A watan Afrilu, 2014, mayakan Boko Haram suka sace yan matan makarantar Chibok sama da 100 a jihar Borno

Borno - Rundunar sojin Bataliya ta 114 da ke Bita a jihar Borno ta samu nasarar ceto ɗalibar makarantar Chibok, wacce yan ta'adda suka sace tare da yan uwanta ɗalibai shekaru 9 da suka gabata.

Leadership ta rahoto cewa ɗalibar yar kimanin shekara 26 a duniya mai suna Hauwa Maltha, ta kubuta daga hannun yan ta'addan Boko Haram a wani samame da Sojoji suka kai Lagara.

Dalibar Chibok.
Sojoji Sun Ceto Dalibar Makarantar Chibok Dauke da Juna Biyu Hoto: leadership
Asali: UGC

Dakarun sojin sun ceto Hauwa tare da ɗiyarta 'yar shekara uku yayin da suka fita Operation a yankin Lagara ranar 21 ga watan Afrilu, 2023, shekaru 9 bayan garkuwa da ita.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Mummunan Hatsari Ya Rutsa da Ɗaliban Jami'a a Najeriya, Rayuka Sun Salwanta

Hauwa ta fito daga ƙabilar Kibaku da ke garin Jila, ƙaramar hukumar Chibok a Borno. Ranar 14 ga watan Afrilu, 2014, mayakan Boko Haram suka shiga makaranta suka kwashi ɗalibai mata da yawa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Lokacin da take hannun 'yan ta'adda, Hauwa ta Auri ɗaya daga cikinsu mai suna Salman, mai ɗaukar hoton tsohon shugaban Boko Haram, Abubakar Sheƙau.

Bayan aurensu, Salman ya rasa rayuwarsa a Tafkin Chadi. Daga nan suka ƙara aurar da Hauwa ga wani mai suna, Mallam Muhammad a Gobara, kuma ta haifa masa yara biyu.

Mijinta na biyu, Mallam Muhammad, ya mutu a sansanin 'yan ta'adda da ke Ukuba a cikin fitaccem Jejin nan Sambisa lokacin artabu tsakanin Boko Haram da ISWAP.

Tun lokacin da Sojoji suka ceto Hauwa ɗauke da juna biyun watanni Takwas da mako biyu, sun kaita Asibiti ana bincikar lafiyarta tare da jaririn cikinta, kamar yadda Sahara Reporters ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Shugaba Buhari Ya Kara Ɗage Kidayar 2023 da Aka Shiya Yi a Najeriya

Bayan kammala duk gwaje-gwajen da ya kamata, Sojojin zasu miƙa Hauwa da ɗiyarta mai suna Fatima hannun gwamnatin jihar Borno domin ɗaukar mataki na gaba.

Gobara Ta Babbake Wani Sashin Fadar Mai Martaba Ooni na Ife

A wani labarin kuma Wani Abu Ya Fashe, Wuta Ta Babbake Fadar Fitaccen Sarki Mai Martaba a Najeriya

Mai magana da yawun fadar Sakin Ife, ya ce lamarin ya faru ne bayan ɗaya daga cikin haɗe-haɗen kayan wutar lantarki ya fashe a sashin fadar.

Tuni dai jami'an hukumar kashe gobara da taimakon ma'aikatan fada da sauran jama'ar gari suka kashe wutar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262