Na Kirkiri Masarautun Kano Ne Don Su Zauna Daram, Ganduje Ya Yi Martan Ga Kwankwaso
- Gwamnan jihar Kano, Ganduje ya bayyana martaninsa game da kamalan da dan takarar shugaban kasa na NNPP ya yi kan masarautun Kano
- Gwamnan ya ce, babu mai ture masarautun Kano guda biyar da ya karkasa a lokacin mulkinsa na tsawon shekaru takwas
- A baya, Kwankwaso ya yi bayani game da makomar masarautun, inda yace Abba Gida-Gida ne ke da ta cewa game dasu
Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya ce, bai kirkiri karin masarautun Kano guda hudu a gwamnatinsa don a rushe su ba.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a bikin ranar ma’aikata a filin wasanni na Sani Abacha da ke Kano, inda yace Allah ba zai turo wanda zai wargaza su ba.
Gwamnatin jihar Kano a baya ta rarraba masarautun Kano zuwa gida biyar, inda daga baya Ganduje ya tsige Muhammadu Sanusi II daga karagar mulkin Kano.
A wani bidiyon da aka gani yana yawo a kafar sada zumunta, sanata Rabiu Musa Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa na NNPP ya ce sabon gwamnan jihar ne ke da ta cewa game da sayadda sarautar Kano ke gudana.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kuma bayyana cewa, kirkirar masarautun guda hudu kari kan masarautar Kano daya ta baya alama ce mai nuna hadin kai, ci gaba da zaman lafiyar al'ummar Kano.
Ganduje ya yi magana game da masarautun Kano
“Na tabbata, kowanne daga cikinku idan ya je hedkwatar wadannan masarautu za ka tabbata cewa babu shakka an kawo ci gaba ga wadannan wuraren.
“Saboda haka, muna tabbatar muku, wadannan masarautun an yi su ne domin ba da hadin kai, wadannan masarautun an yi su ne domin ci gaba, wadannan masarautun an yi su ne domin tarihi, wadannan masarautun an yi su ne domin daraja sarautar gargajiya, wadannan masarautun an yi su ne domin daraja wadannan mutanen da ke zaune a wadannan wuraren.
“Kuma ina tabbatar muku, wadanann masarautun, dindindin sun zo da zama da gindinsu. Idan Allah ya yarda sai Mahdi ka ture, kuma Mahdin da zai ture Allah ba zai kawo shi ba.
“Kuma ina tabbatar muku ko ba ma gwamnati, muna nan muna addu’a Allah ya zaunar da wadannan masarautun.”
A baya Kwankwaso ya yi ishara ga makomar masarautun kano guda biyar da aka karkasa a gwamnatin Ganduje.
Asali: Legit.ng