Batun Janye Sabbin Takardun Kudi, CBN Ya Bayyana Gaskiyar Zance
- Babban bankin Najeriya (CBN), ys fito fili ya musanta rahotannin cewa yana shirin janye sabbin takardu kuɗi
- Babban bankin ya ce baya da shirin yin hakan, inda ya yi kira ga mutane da su yi watsi da rahotannin
- Babban bankin ya tabbatar da cewa a sabbin takardun kuɗin da tsaffi za su cigaba da aiki tare har zuwa lokacin wa'adin da za a janye tsaffin kuɗin
Abuja - Babban bankin Najeriya (CBN) ya yi fatali da rahotannin da ke yawo cewa yana duba yiwuwar janye sabbin takardun kuɗin N1000, N500 da N200 da aka sauyawa fasali.
Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa babban bankin ya musanta wannan jita-jitar ne, a wata sanarwa da darektan riƙo na sashin watsa labarai, Dr. Isa Abdulmumin, ya fitar.
Sanarwar na zuwa ne bayan rahotanni sun yaɗu kan cewa babban bankin, na duba yiwuwar janye sabbin takardun kuɗin daga hannun mutane, cewar rahoton Premium Times.
Sanarwar na cewa:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Muna son mu bayyana cewa wannan jita-jitar ba ta da tushe ballantana makama, sannan wani shiri ne na wasu kawai masu son sanya tsoro a zukatan al'umma. Sabbin takardun kuɗin da tsaffi na cigaba da yaɗuwa a tare."
"Bankin CBN na cigaba da samun sabbin takardun kuɗin daga hannun kamfanin buga kuɗi na Najeriya (NSPMC)."
Abdulmumin ya ce CBN a shirye ya ke ya samar da kuɗin da aka yarje domin wanzuwar tattalin arziƙin ƙasa.
"Saboda haka muna kira ga mutane da su yi watsi da rahotannin da ke nuni da cewa, za a janye sabbin takardun kuɗin."
"Domin cire dukkanin wani shakku, za a cigaba da amfani da sabbin takardun kuɗin da tsaffi a matsayin halastattun kuɗi."
"Za su cigaba da yawo tare domin cinikayya har zuwa ranar 31 ga watan Disamban 2023, lokacin da tsaffin takardun kuɗin N1000, N500 da N200, za a janye su gabaɗaya." A cewarsa.
Arzikin Abdul Samad Rabiu Ya Karu da $600m, Ya Zama Attajiri na 3 a Fadin Afrika
A wani rahoton na daban kuma, kun ji cewa shahararren attajirin na Najeriya, Abdul Samad Rabiu, ya samu ƙarin arziƙin $600m.
Attajirin yanzu ya ƙara matsawa a cikin jerin mutanen da suka fi kowa kuɗi a Nahiyar Afrika.
Asali: Legit.ng