Yaron Sanusi II Ya Fadi Ainihin Laifin Mahaifinsa da Ya Jawo Ganduje Ya Tsige Shi
- Mutane sun dawo da batun tsige Muhammadu Sanusi II da aka yi daga gadon sarauta a 2020
- Ashraf Sanusi yana da ra’ayin cewa babu wani laifi da mahaifinsu ya aikata, illa sukar Gwamnati
- A matsayinsa na jinin sarauta, matashin ya ce tofa albarkacin baki kan tattalin arziki bai saba doka ba
Kano - Har yanzu ana ta surutu a game da tunbuke Muhammadu Sanusi II da aka yi daga kan mulki a farkon 2020 da kishin-kishin din maida shi mulki.
Wani Bawan Allah mai suna Asad Mukty a dandalin Twitter, ya nemi a fada masa laifin da Mai martaba Muhammadu Sanusi II ya aikata, aka tsige shi.
Jama’a sun yi ta tofa albarkacin bakinsu, su na ba shi amsa, kusan wanda ya fi daukar hankali shi ne wanda ya fito daga bakin Malam Ashraf Sanusi.
Ga asalin tambayar da aka jefa:
“Shin wani zai iya tunatar da ni game da abin da ya jawo aka tunbuke Sanusi Lamido Sanusi daga sarautar Kano? Ina neman kakkarfan dalili da hujja don Allah.”
Ashraf Sanusi ya bada amsa
Adam Sanusi (Ashraf) yana cikin ‘ya ‘yan Sarkin Kano na 14, Malam Muhammadu Sanusi II.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ashraf Sanusi ya ce ba komai ne ya jawo mahaifin na su ya rasa rawaninsa ba sai saboda yana sukar Gwamnatin Mai girma Abdullahi Umar Ganduje.
“Ya soki gwamnati” tamkar laifi ne ga masanin tattalin arzikin da ya fi kowa a jihar ya fadi abin da yake ransa a game da tattalin arziki.
- Adam Sanusi
Sauran amsoshin da mutane su ka bada
"An sauke shi ne saboda raina gwamnatin Kano, yana yi tamkar mai mulkin Kano, kuma ya jefa kan shi a kan abubuwan da ba su shafi masarauta ba. Na karshe kuma shi ne ya ruguza al’adar Kanawa mai tarihi. Nagode."
- Talban Illela
Ya cika surutu a kan abubuwan da ba su cancanta. Mutumin yana da matukar ilmi, amma wasu lokutan masu ilmi ba su dacewa da shugabanci, dalili kuwa su na raina mutane, kuma su na jin sun fi kowa sani.
- Kargi Abdullahi
Shi kuma wani ya ce an sauke shi ne saboda yawan zubansa watau surutu, ya ce hakan bai dace da Sarki ba.
Aminu Dahiru Gurama yana ganin Sanusi II ya jefa kan shi a siyasa ne, hakan ya jawo masa matsala.
Doguwa ya shiga takara
Dazu nan labari ya zo cewa Hon. Alhassan Ado Doguwa zai nemi Shugabancin Majalisa bayan lashe zabe a karo na 5 a jere, a wannan karo ya doke NNPP.
Yusuf Gagdi, Tajudeen Abbas, Aminu, Idris Wase, Ben Kalu, Muktar Betara, Sada Soli, Tunji Olawuyi da Abubakar Makki su na harin wannan kujera a APC.
Asali: Legit.ng