Gwamnan Jihar Nasarawa Ya Halarci Auren Dansa a Amurka, Hotuna Sun Bayyana
- Zakari Sule, da a wajen gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya angwance da masoyiyarsa a wani kasaitaccen biki
- An daura auren Zakariya da amaryarsa mai suna Alysa a ranar Asabar, 30 ga watan Afrilu a McKinney Roughs Nature Park, Texas, kasar Amurka
- Gwamnan da wasu hadimai da makusantansa sun samu halarctan bikin wanda aka yi shi a saukake da makusanta
Dan Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa, Zakari Sule, ya angwance da sahibarsa, Alysa a kasar Amurka.
Jaridar Daily Nigerian ta rahoto cewa ma'auratan sun shiga daga ciki ne a wani dan kwarya-kwaryan biki da aka yi a ranar Asabar a McKinney Roughs Nature Park, Texas, kasar Amurka.
Angon shine babban dan matar gwamnan ta biyu mai suna Ijim Sule.
Gwamnan ya samu rakiyar wasu hadimai da makusantansa zuwa wajen daurin auren.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai Tanimu Sarki, kwamishinan filaye; Yusuf Maianguwa, babban mai ba gwamnan shawara kan hulda da jama'a, Abuja da wani Aliyu Tijani.
Da yake wallafa hotunan auren a shafin Facebook, babban sakataren gwamnan jihar, Ibrahim Addra, ya rubuta:
"Ina tayaku murna Alysa & Zakari Sule a ranar aurensu a McKinney Roughs Nature Park, 1884 State Highway 71, Cedar Creek, TX 78612.
"Mai girma Injiniya Abdullahi A. Sule da rakiyar wasu jami'an gwamnati da abokansa, sun halarci bikin."
Uba ya fashe da kuka a wajen shagalin bikin diyarsa
A wani labari na daban, wani uba ya tsuma zukatan mutane da dama a soshiyal midiya bayan ya fashe da kuka a yayin da ake tsaka da shagalin bikin kyakkyawar diyarsa da sahibin ranta.
Uban amaryar ya kalli kwayar idanun diyarsa yayin da suke filin biki nan take sai hawaye ya fara kwaranya daga idanunsa wanda ke nuna yana kewa da tausayin diyar tasa yayin da take shirin barin gidansa zuwa ga nata gidan.
Mutane da dama da suka yi martani a soshiyal midiya sun jinjinawa irin soyayyar da ke tsakanin 'ya'ya mata da iyayensu maza harma wasu suka ce idan mahaifinsu ya yi kuka ranar aurensu babu inda za su sai dai a hakura a dage auren zuwa wani lokaci.
Asali: Legit.ng