Ban Aikata Wani Laifi Ba, Jami’in REC Na INEC a Adamawa da Aka Dakatar Ya Yi Bayani Game da Zaben Jihar
- Kwamishinan zaben jihar Adamawa ya bayyana gaskiyar yadda zaben gwamnan jihar ya kasance
- A cewarsa, wasu kwamishinonin INEC na kasa sun karbi cin hanci a hannun gwamnan jihar, Ahmadu Fintiri
- Wannan na fitowa ne daga inda Ari ke boye yayin da jami'an tsaro ke ci gaba da neman inda yake
Najeriya - Dakataccen Kwamishinan Zabe (REC) a jihar Adamawa, Hudu Yunusa-Ari, ya ce ya ayyana 'yar takarar jam’iyyar APC a matsayin wacce ta lashe zaben gwamnan jihar ne domin ceto tsarin dimokuradiyya.
Ari ya ce ya yi aiki ne bisa ga ikon da dokar zabe ta ba shi a matsayinsa na babban jami’in tattara sakamakon zabe a jihar Adamawa, The Nation ta ruwaito.
Bayan nasa na kunshe ne a cikin wata wasika mai shafuka hudu da ya rubuta ya mika wa babban sifeton ‘yan sandan daga inda yake boye.
Manyan jami'ai biyu sun karbi cin hanci daga Fintiri, inji Ari
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Hakazalika, ya zargi kwamishinonin INEC na kasa biyu da aka tura jihar domin sa ido kan zaben da aka karasa a ranar 15 ga watan Afrilu da karbar cin hanci daga gwamna Ahmadu Fintiri domin alanta shi a matsayin wanda ya lashe zaben.
A cikin wasikar mai dauke da kwanan watan Afrilu 20, Ari da har yanzu ake takaddama kan aikinsa, ya kuma zargi kwamishinonin biyu da dauke nauyin da ya rataya a wuyansa na REC a jihar.
Abin da na aikata daidai ne
Ya musanta aikata ba daidai ba wajen ayyana Aishatu Dahiru (Binani) a matsayin wacce ta lashe zaben gwamna inda ya ce abin da ya yi daidai yake da hakkin da dokar zabe ta dora masa a matsayin kwamishinan zabe na jihar.
Ya ce a matsayinsa na Babban Jami’in tattara zaben jihar, ya lura cewa sakamakon da aka dora a tashar IREV ba shi ne ya sa hannu akai ba, don haka ba sahihi bane, rahoton Daily Trust.
Har yanzu dai Ari bai bayyana ba, kuma ana ci gaba da neman inda yake don yi masa titsiye game da ayyukansa na zaben gwamnan Adamawa.
A baya, shugaba Buhari ya ce a gaggauta kamo Hudu Ari tare da bincikarsa da kuma hukunta shi idan ya aikata laifi.
Asali: Legit.ng