Likitocin Najeriya Sun Ba Buhari Wa’adin Makwanni 2 Don Fara Aiwatar da Yajejeniyar da Suka Kulla
- Kungiyar likitoci a Najeriya ta yi barazanar yin yajin aiki idan gwamnati bata biya musu bukatunsu da suka gabatar ba
- Kungiyar na neman a fara ware 15% na kasafin kudin Najeriya tare da tura shi ga fannin lafiya saboda wasau dalilai
- Hakazalika, suna neman a kara albashin ma’aikata likitoci da 200% na adadin kudin da ake biyan likitocin kasar a yanzu
Abeokuta, jihar Ogun - Alamu na nuna kasar nan za ta rikice da yajin aikin likitoci idan gwamnatin Buhari bata gaggauta daukar mataki cikin kankanin lokaci ba.
Wannan zai faru ne sakamakon gargadin da kungiyar likitoci masu neman kwarewa ta Najeriya ta yi na cewa, gwamnatin ta gaggauta fara aikwatar da yajejeniyar da suka cimma a baya.
A cewar rahoton da muka samo, kungiyar ta ba da makwanni biyu a matsayin wa’adin da gwamnati ya kamata ta fara aiwatar da bukatunsu.
A makon da ya gabata, kungiyar ta yi taro a babban asibitin tarayya da ke Abeokuta ta jihar Ogun, inda anan ne ta bayyana wannan garggadin.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Meye suke bukata?
A cewar rahoton gidan talabijin na Channels, likitocin na neman gwamnati take ware 15% cikin 100% na kasafin kudin shekara ga fannin lafiya.
A baya gwamnatin na ware 15% ne kacal ga fannin lafiya a duk kasafin da ke fita a shekara, kamar yadda rahotanni suka bayyana.
A cewar kungiyar, sanya 15% ga fannin ne zai magance matsaloli da yawa da ma’aikatan lafiya ke fuskanta a halin da ake ciki.
Matsalolin da suka yiwa fannin katutu
Daga cikin matsalolin da kungiyar ta fitar tace sun yiwa ma’aikatar lafiya da fannin katutu akwai rashin daukar ma’aikatan da za su maye gurbin da ake dashi a fannin.
A bangare guda, kungiyar ta bayyana bukatar a yi gyara ga albashin ma’aikatan kiwon lafiya cikin gaggawa, inda suke bukatan karin 200% na albashin likitoci na yanzu, rahoton BBC News.
Ba yau aka fara ba, kungiyar likitocin na kai ruwa rana da gwamnatin tun shekarun baya, inda yanzu bukatar a sake albashin mambobinta da aka rikci a shekarun 2014, 2015 da 2016.
A wani labarin, kunji yadda gwamnati ta ware ranar Litinin mai zuwa domin yin murnar ranan ma’aikata, inda ta ba da hutun kwana daya ga ma’aikatan kasar.
Asali: Legit.ng