'Yan Bindiga Sun Kashe Wani Soja, Sun Yi Awon Gaba da Abokin Aikinsa a Jihar Nasarawa

'Yan Bindiga Sun Kashe Wani Soja, Sun Yi Awon Gaba da Abokin Aikinsa a Jihar Nasarawa

  • An samu tsaiko a jihar Nasarawa yayin da wasu ‘yan bindiga suka sace wani soja tare da kashe abokin aikinsa a kan babur
  • Gwamnatin jihar Nasarawa ta mika sakon ta’aziyya ga rundunar sojin jihar bisa wannan mummunan rashin da aka yi
  • Jihohin Arewa na ci gaba da fuskantar harin ‘yan bindiga, a makon nan ne wasu tsagerun ‘yan bindiga suka bindige matasa biyu

Jihar Nasarawa - Wasu ‘yan bindiga a jihar Nasarawa sun hallaka soja tare da sace abokin aikinsa, inda suka bar babur din da sojojin ke kai a hanyarsu ta zuwa sansanin soja na Idadu kusa da Ibbabu-Idadu a karamar hukumar Doma ta jihar.

Wata majiyar soja da ta nemi a sakaya sunanta ta shaidawa Daily Trust cewa, sojan da aka kashe yana tare da abokin aikinsa ne lokacin da aka farmake su kana aka hallaka shi.

Kara karanta wannan

Karshen alewwa: 'Yan bindiga sun gamu da ajali yayin da suka zo sce fitaccen dan kasuwa a Arewa

A cewar wata majiya, ‘yan bindigan na yawan addabar manoma da ‘yan kasuwa da ranan Allah a yankin na Ibbabu-Idadu, inda suke sace kayayyaki tare da keta hakkin mata.

Yadda 'yan bndiga suka kashe soja a Nasarawa
Jihar Nasarawa da ke Arewacin Najeriya | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

An shiga tashin hankali bayan faruwar harin

Jaridar ta kuma bayyana cewa, sojan da aka kashen dan asalin jihar Gombe da ke aiki a sansanin sojojin Idadu a karamar hukumar Doma, Street Reporters ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“’Yan bindigan sun farmaki marigayin ne da gatari sannan suka jefa babur dinsa a tafkin da ke gefen hanya. An sace abokinsa sannan an tafi dashi wani wurin da ba a sani ba.
“Mummunar mutuwar jami’in sojan ya kunna wutar rikici a yankin Doma da kewaye ciki har da yankin Yelwa Ediys, Igbobo Idadu, Opkatta Rukubu Akpanaja, Doka, Ajimaka, Okpanya kasancewar manoma ba za su samun damar zuwa gona.”

Kara karanta wannan

Innalillahi: 'Yan bindiga sun kashe yaran da suka sace a Arewa, sun sako wasu 70

Majiyar sojan kuwa ta ce, yanzu haka jami’an tsaro sun fara aikin kakkabe yankin tare da kokarin gano maboyar ‘yan ta’addan.

Gwamnatin Zamfara ta mika sakon jaje

A bangare gida, mataimakin gwamnan jihar Nasarawa, Dr. Emmanuel Akabe ya mika sakon ta’aziyya ga kwamandan rundunar ta 4 ta Special Force da ke Doma, Manjo Janar O.O Soyele bisa faruwar lamarin.

Ya kuma yi Allah wadai da kisan sojan, inda yace hakan babban rashi ne ga rundunar sojin Najeriya da ma kasar baki daya.

A nasa bangaren, Manjo Janar Soyele ya yaba wa gwamnnatin jihar bisa yiwa rundunar jaje, inda yace yanzu haka rundunar na ci gaba da aiki tukuru don kawo ceto wanda aka sacen.

A jihar Zamfara kuwa, wasu ‘yan bindiga sun hallaka matasa biyu da suka sace tare da sako wasu 70 da suka sace tare dasu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.