'Yan Sanda Sun Sheke ’Yan Bindiga 2 a Lokacin da Suka Yi Yunkurin Sace Dan Kasuwa a Katsina
- ‘Yan sandan jihar Katsina sun yi nasarar sheke wasu ‘yan bindigan da suka nufi sace wani dan kasuwa a jihar
- Wannan ya faru ne a lokacin da tsagerun ke kokarin sace wani dan kasuwa a jihar da ke Arewa maso Yamma
- An bangare guda, wasu tsagerun ‘yan bindiga sun harbe matasa biyu a jihar Zamfara bayan sace su a daji
Jihar Katsina - Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina a jiya Juma’a tace jami’anta sun dakile wani mummunan hari tare da kashe wasu ‘yan ta’adda biyu.
Wannan na fitowa ne daga bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, CSP Gambo Isah, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.
A cewarsa, jami’an sun dakile harin ne bayan samun bayanan sirri na yadda ‘yan ta’addan ke kokarin sace mutane.
Ya kara da cewa, bayanan na sirri sun kai ga jami’an Anti-Kidnapping Unit suka lallasa gungun ‘yan bindigan da suka dade a jadawalin nema na jami’an tsaro.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
‘Yan bindiga na kokarin sace dan kasuwa, sun bakunci kiyama
Ya kuma bayyana cewa, an dakile harin ne a lokacin da tsagerun ke kokarin sace wani fitaccen dan kasuwa a jihar.
A cewar sanarwar, an gano gawar wani kasurgumin dan bindigan da ake zargin yana da hannu a wani harin da aka kai a 2020 a karamar hukumar Malumfashi ta jihar Katsina, rahoton This Day.
A cewar wani yankin sanawar:
“An kashe ‘yan bindiga biyu an kuma kwace bindigogi kirar AK-47.
“A wurin da lamarin ya faru, an ga gawar wani Samaila Shehu da kauyen Tsaunin Kura, a karamar hukumar Malumfashi, fitaccen dan bindigan da aka kama a 2020 da hannu a harin makarantar ma’aikata ta GSS Malumfashi, Katsina kuma aka gurfanar dashi a kotu.”
An kashe yara 2, an sako 70 cikin 85 da aka sace a Zamfara
A wani labarin, kunji yadda aka sace wasu yara a jihar Zamfara, inda daga baya aka sako su bayan karbar kudin fansa.
An kuma ruwaito cewa, an kashe biyu daga cikin yaran da aka sacen, wanda daga baya aka sako 70 cikin 85, inji rahoton majiya daga jihar.
Ya zuwa yanzu, ‘yan sandan jihar Zamfara basu ce komai game da wannan lamarin ba, amma majiya ta tabbatar.
Asali: Legit.ng