'Yan Sanda Sun Halaka 'Yan Ta'adda Mutum 2 a Jihar Katsina
- Wasu miyagun ƴan ta'adda mutum biyu sun gamu da ajalin su a hannun ƴan sanda a jihar Katsina
- Ƴan ta'addan suna kan hanyar su ne ta zuwa sace wani ɗan kasuwa a jihar lokacin da suka yi karon batta da ƴan sandan
- Rundunar ƴan sandan jihar ta samo gawar ɗaya daga cikin wanda ya daɗe yana aikata ta'addanci a jihar
Jihar Katsina - Ƴan sanda a jihar Katsina sun samu nasarar halaka wasu mutum biyu da ake zargin ƴan ta'adda ne, sannan suka kwato bindigogi 2 ƙirar AK 47 a hannun su.
Jaridar Channels tv yace ƴan ta'addan sun gamu da ajalin su ne lokacin da suke kan hanyar su ta zuwa sace wani sanannen ɗan kasuwa a jihar.
Lamarin ya auku ne ranar Alhamis da rana bayan sashin rundunar ƴan sandan da ke yaƙi da ayyukan garkuwa da mutane ya samu bayanan sirri akan ƴan ta'addan.
A yayin duba wajen da akayi musayar wuta tsakanin jami'an tsaro da ƴan ta'addan, an samu gawar wani mai suna Sama'ila Shehu, na ƙauyen tsaunin Kura cikin ƙaramar hukumar Malumfashi ta jihar Katsina.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Shehu wani gawurtaccen ɗan ta'adda ne wanda aka taɓa kama wa yana da hannu a harin da aka kai a gidajen malaman makarantar GSS Malumfashi, a shekarar 2020 sannan aka miƙa shi zuwa kotu a lokacin.
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Katsina, CSP Gambo Isah, a cikin wata sanarwa ranar Juma'a ya bayyana cewa, ana cigaba da gudanar da bincike, sannan za a gabatar da cikakken rahoto idan aka kammala binciken.
Yan Bindiga Sun Sako Kwamishiniyar Hukumar NPC a Jihar Rivers
Da zu mun kawo rahoto kan cewa ƴan bindiga sun sako kwamishiniyar hukumar ƙidaya ta ƙasa da suka ƙwamushe a jihar Rivers, bayan kwashe kwanaki a hannun su.
Bayin Allah Da Dama Sun Jikkata, Dukiyoyi Sun Salwanta a Wani Mummunan Fada Da Ya Barke a Jihar Arewa
Mrs Gloria Izonfuo, kwamishiniyar hukumar NPC ta jihar Bayelsa, ta faɗa koma ƴan bindiga ne, bayan sun sace a jihar Rivers, lokacin da ta ke dawowa daga wata tafiya da ta yi.
Sai da kwamishiniyar ta kwashe kwanaki 5 a hannun ƴan bindigan kafin su sako ta.
Asali: Legit.ng