Mutum 10 Sun Mutu Yayin da Wata Tanka Ta Fashe a Jihar Filato
- Wata Tankar dakon man fetur ta fashe a Jos, babban birnin jihar Filato, ta yi ajalin mutane 10
- Bayanai sun nuna cewa Tankar maƙare da man Fetur ta kucce wa direban kana ta fashe kuma ta kama da wuta ta kona mutanen ƙurmus
- Rundunar yan sandan jihar Filato ta tabbatar da faruwar lamarin da cewa ta tura jami'ai wurin don gano illar da hatsarin ya haifar
Plateau - Wasu mutane 10 da har yanzun ba'a gano bayanansu ba sun kone ƙurmus a mahaɗar titunan Bauchi Junction da ke Jos, babban birnin jihar Filato.
Channels tv ta rahoto cewa mutanen sun ƙone ne yayin da Tanka maƙare ɗa man Fetur ta kucce kana ta yi tunguragutsi daga bisani ta fashe kamar tashin Bam, ta kama da wuta.
Wane mataki jami'an tsaro suka ɗauka?
Bayin Allah Da Dama Sun Jikkata, Dukiyoyi Sun Salwanta a Wani Mummunan Fada Da Ya Barke a Jihar Arewa
Rundunar 'yan sanda reshen jihar Filato da ke arewa ta tsakiya a Najeriya ta tabbatar da faruwar lamarin kuma ta tura jami'ai.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cewar rundunar 'yan sandan ta tura jami'anta na musamman zuwa wurin da ibtila'in ya faru domin su gano yawan asarar da hatsarin ya haifar.
Ta ce bayan zuwan jami'an yan sanda ne aka ɗauki waɗanda lamarin ya rutsa su zuwa Asibitin Filato na musamman yayin da kuma aka ci gaba da kokarin saita komai.
"Daga isar jami'ai wurin da abun ya faru suka ɗauki gawarwakin mutanen da haɗarin ya rutsa da su zuwa Asibiti na musamman a jihar Filato suka aje su. A halin yanzun aikin ceto ya ci gaba gadan-gadan," inji rundunar yan sanda.
Legit.ng Hausa ta fahimci cewa wannan fashewa ta Tankar dakon man Fetur ta shafi motoci Uku da kuma Babur mai taya uku watau Napep guda 2 a kan titin.
Wurin da haɗarin ya auku babbar mahaɗa ce da ke haɗa cunkoso kuma titin ne ke kai matafiya zuwa shiyyar arewa maso gabashin ƙasar nan, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Yan bindiga sun kashe babban mutum a Imo
A wani labarin kuma Yan Bindiga Sun Kutsa Kai Ɗaƙin Taro, Sun Kashe Shugaban Al'umma
Miyagun yan bindiga da ba'a sannko su waye ba sun kashe shugaban al'umma, Chief Monday, a jihar Imo.
Mamacin na tsaka da jawabi ga jama'a a ɗakin taro maharan suka harbe shi har lahira a jihar da ke kudu maso gabashin Najeriya.
Asali: Legit.ng