DSS Ta Tsare Hadimin Fintiri Da Magoya Bayan PDP Kan Kai Wa Ma'aikatan INEC Hari

DSS Ta Tsare Hadimin Fintiri Da Magoya Bayan PDP Kan Kai Wa Ma'aikatan INEC Hari

  • Hukumar DSS ta kama wasu magoya bayan PDP bisa rikicin da ya biyo bayan sanarwar rudani da ta bayyana Binani a matsayin wadda ta lashe zabe a Jihar Adamawa
  • Cikin wanda hukumar ta tsare akwai mai kula da tsaron gwamnan jihar, Ahmadu Fintiri da wasu mutane uku
  • Hukumar ta tsare mutanen tsawon kwanaki sai dai an kasa jin ta bakinta dangane da lamarin

Adamawa - Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS) ta cafke shugaban jami'an tsaron gwamnan Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, bisa zargin cin zarafin jami'an zabe da wani babban jami'in tsaro, Daily Trust ta rahoto.

Wasu gungun yan daba sun balle zuwa otal din Green City Yola suka fito da wasu jami'an daga dakinsu bayan sanarwar rudani da ta bayyana yar takarar APC, Sanata Aishatu Dahiru Binani, a matsayin wacce ta lashe zaben da dakataccen Kwamishinan zaben jihar (REC), Barista Hudu Yunusa Ari ya bayyana.

Kara karanta wannan

Matar Aure Ta Taka Rawa Da Girgiza Yayin da Uwar Mijinta Ta Kai Masu Ziyara, Ta Kawo Masu Abinci Da Yawa

Ma'aikatan DSS
DSS Ta Kama Jam'in Tsaron Fintiri, Magoya Bayan PDP Saboda Farmakar Jami'in INEC. Hoto: The Punch
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta ya nuna wani dattijo Farfesa Zuru, daya daga cikin kwamishinonin zabe da hukumar ta tura don kula da zaben cike gurbi a jihar, ana cin zarafinsa.

An ruwaito mai tsaron gwamnan, Ahmad Umar, yana cin zarafin babban jami'in mai suna Halilu wanda ke dakin otal din lokacin da ya jami'in yazo tare da rakiyar wasu yan sandan gidan gwamnati da kuma tawagar matasa kafin daukarsa zuwa wani wajen.

Bidiyon jami'in da aka yaga wa kaya wasu na masa tambayoyi an watsa shi a shafukan sada zumunta, abin da wasu ke gani a matsayin cin zarafi ga hukumar yan sandan sirri.

Hukumar ta kuma kama akalla magoya bayan jami'yyar PDP a mabambantan wurare bisa zargin hannu a harin.

Shugaban PDP na Jihar Adamawa ya jagoranci zanga-zanga don a saki mambobinsu da aka kama

Kara karanta wannan

Zargin Kisan Kai: Doguwa Ya Shiga Matsala Yayin Da Kotu Ta Ba Atoni Janar Na Jihar Kano Sabon Umurni

Shugaban PDP na jihar, Barista Tahir Shehu, ya jagoranci zanga-zanga a ofis din DSS da ke Yola ranar Laraba don bukatar a saki mutum ukun da aka tsare.

"Mun fito da yawanmu don gudanar da zanga-zangar lumana saboda a saki magoya bayan jam'iyyarmu da aka tsare tsawon kwanaki ba tare da an kai shi kotu ba duk da takardar da muka rubuta ga daraktan DSS na Jihar Adamawa, muka rokon da ya bar wanda ke tsare su gana da lauyoyinsu da iyalansu saboda ya saba da doka a tsare mutum na sama da awa 24 ba tare da kai shi kotu ko hana shi ganawa da iyalansa," in ji Shehu.

A daya bangaren, wata babbar kotu karkashin jagorancin mai shari'a Christopher Dominic Mapeo ta bada umarni ranar Alhamis ga hukumar DSS ta saki mutum uku da ta tsare ba tare da bata lokaci ba.

Kotu ta bada umurnin DSS ta fito da yan PDP da aka tsare a Jihar Adamawa

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotun tarayya ta yanke hukunci kan karar da Binani ta shigar game da zaben Adamawa

A wani rahoton kuma kun ji cewa babban kotu a jihar Adamawa ta bada umurnin hukumar DSS ta sako yan PDP guda uku da aka tsare.

Mai shari'a Christopher Mapeo ya ce idan har DSS ta cigaba da tsare su ta saba doka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164