Gwamnati Ta Tsaida Ranakun Bude Titunan Kano-Zaria-Kaduna, Legas-Ibadan, da Gadar Neja
- Nan da tsakiyar watan Mayu, za a iya kaddamar da titin Kano-Zaria da kuma na Zaria-Kaduna
- Kafin nan, ‘Yan kwangila za su mikawa gwamnatin tarayya hanyar Legas-Ibadan da aka fadada
- Haka zalika za a bude gadar Neja kafin Muhammadu Buhari ya sauka daga mulki a karshen Mayu
Abuja - Ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed ya ce ‘yan kwangilan da ke hanyoyin Kano-Zaria da Zaria-Kaduna sun kusa gama aikinsu.
Kamar yadda rahoto ya zo a Daily Trust, Alhaji Lai Mohammed ya ce za mikawa gwamnati wadannan tituna da gadar Neja a ranar 15 ga Mayu.
Mai girma Ministan ya yi wa manema labarai bayanin nan bayan kammala taron majalisar Ministoci na FEC a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Lai ya shaida cewa a ranar 30 ga watan Afrilun nan za a mika masu babban titin Legas-Ibadan mai tsawon kilomita 116 da gwamnatinsu ta fadada.
Gadar Neja ta ci Biliyoyi
A kwangilar gadar Neja ta biyu, rahoton ya nuna an kara N1.398bn a kudin kwangilar a dalilin karasa aikin wani bangare na gadar Uto a jihar Delta.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Gadar mai tsawon kilomita 2.6 da ta ratsa garin Ikenke ta jawo kudin kwangilar da gwamnatin tarayya ta biya ya karu daga N4.435bn zuwa N5.835bn.
Wasu ayyuka da aka karasa
Ministan ya ce an gama gadar Loko-Oweto, haka zalika gadar Ikom da sakatariyoyin gwamnatin tarayya da ke Nasarawa, Awka, Bayelsa da Zamfara.
Komai ya kammala wajen gina gidaje 700 a Zuba, abin da ya rage shi ne a kaddamar da su.
Sun ta rahoto Ministan labaran kasar yana mai farin cikin bada sanarwar karkare titin Kano-Zariya mai 137km da Zaria-Kaduna mai tsawon 73km.
FEC ta amince da kudin wasu ayyuka
A jawabinsa, karamin Ministan ilmi, Goodluck Opiah ya shaida cewa majalisar FEC ta amince a kashe N32.4bna karasa babban dakin karatu na kasa.
Ministan gona ya ce an yi na’am da fara kashe N6bn a gina wani wuri da za a kira gidan noma.
Jibrin a gidan Tinubu
Ku na da labari mutane sun rasa me ya kai zababben ‘dan majalisar mazabar Kiru da Bebeji a Jam’iyyar NNPP, Abdulmumin Jibrin wajen Bola Tinubu.
A takarar 2023, Jibrin yana cikin wadanda suke magana da yawun Rabiu Kwankwaso, kwatsam sai ga shi a gidan shugaba mai jiran gado.
Asali: Legit.ng