Jami'ar BUK Ta Yi Babban Tashi, Rijistara Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Jami'ar BUK Ta Yi Babban Tashi, Rijistara Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Allah ya yi wa Rijistaran jami'ar Bayero da ke Kano, Malam Salim rasuwa a farkon awannin yau Laraba 26 ga watan Afrilu
  • Hukumar BUK ta tabbatar da lamarin a wata sanarwa, ta ce wannan babban rashi ne ga baki ɗaya bangaren ilimi a Najeriya
  • Tuni dai aka masa jana'iza a babban Masallacin BUK da misalin ƙarfe 10:00 na safiya

Kano - Rijistara na jami'ar Bayero da ke Kano (BUK), Malam Jamil Ahmad Salim, ya riga mu gidan gaskiya yana da shekaru 60 a duniya.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Malam Jamil Ahmad ya rasu ne a farkon awannin yau Laraba 26 ga watan Afrilu, 2023.

Malam Jamilu Ahmad Salim.
Jami'ar BUK Ta Yi Babban Tashi, Rijistara Ya Riga Mu Gidan Gaskiya Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Hukumar BUK ta tabbatar da lamarin a wata sanarwa da mataimakin shugaban jami'ar, VC, Farfesa Sagir Abbas, ya fitar ranar Laraba da muke ciki.

Kara karanta wannan

Malamin Jami'ar Najeriya A Jihar Arewa Ya Rasu Yana Cikin Barci

A tahoton Daily Nigerian, Sanarwan ta ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Hukumar makaranta ta samu labarin rasuwar Rijistara, Malam Jamilu Ahmad Salim, wanda ya koma ga mahaliccinsa yau Laraba 26 ga watan Afrilu, 2023 bayan gajeruwar rashin lafiya."
"Muna Addu'ar Allah SWT ya gafarta masa kura-kuransa kuma ya sa Aljannatul Firdausi ta zama makoma a gare shi, Ameen."
"Malam Salim, wanda ya shafe shekaru huɗu a matsayin Rijistaran jami'a, mutum ne mai sadaukarwa kuma ma'aikaci mai aiki tuƙuru wanda da gudummuwarsa makaranta ta haɓaka kuma ta ci gaba."

Yaushe za'a masa jana'iza?

Hukumar BUK ta ƙara da cewa za'a sallaci mamacin kana a kai shi ga makwancinsa da misalin ƙarfe 10:00 na safiyar Laraba a babban Masallacin Jami'a, New Campus, Kano.

"Rasuwar Malam Salim babban giɓi ne ba wai ga jami'ar BUK kaɗai ba, baki ɗaya bangaren ilimi a Najeriya ya yi rashi mai girma. Za'a yi kewar jajircewarsa, sadaukarwa da aiki tukuru don ci gaban jami'a."

Kara karanta wannan

Masha Allah An Fara Jigilar 'Yan Najeriya Da Suka Makale a Sudan, Yau Za a Kwaso Da Dama

Da fari, an naɗa marigayi Salim a matsayin muƙaddashin rijistaran BUK ranar 15 ga watan Maris, 2021 daga bisani kuma aka tabbatar masa da matsayin a watan Okotoba, 2021.

Jerin jami'o'in da suka ƙara kuɗin karatu

A wani labarin kuma Mun Tattaro Muku Jami'ar UNIMAID Da Sauran Jami’o’in Tarayya Da Suka Kara Kudin Makaranta

Da yawan jami'o'i a Najeriya mallakin gwmanatin tarayya sun ƙara yawan kuɗin makaranta kan kowane ɗalibi bisa wasu dalilai da suka bayyana.

Ana ganin dai lamarin ƙarin kuɗin zai shafi talaka kai tsaye wanda ke fafutukar samun ilimi domin gyara rayuwarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262