UNIMAID Da Sauran Jami’o’in Tarayya Da Suka Kara Kudin Makaranta

UNIMAID Da Sauran Jami’o’in Tarayya Da Suka Kara Kudin Makaranta

Wasu manyan jami'o'in gwamnatin Najeriya sun kara kudin makarantarsu saboda gazawar kungiyar malaman jami'o'i (ASUU) wajen matsawa gwamnatin tarayya ta samar da karin kudade.

Jami'o'i da dama a fadin kasar sun sanar da karin fiye da kaso 200 na kudin rijista da kudin makarantar dalibai, jaridar Punch ta rahoto.

Kofar shiga jami'ar Maiduguri
UNIMAID Da Sauran Jami’o’in Tarayya Da Suka Kara Kudin Makaranta Hoto: STEFAN HEUNIS/AFP
Asali: UGC

Ga jerin wasu daga cikin jami'o'in da suka kara tsadar kudin makaranta a kasa:

Jami'ar tarayya ta Dutse

Jami'ar tarayya ta Dutse ta sanar da karin kudin makaranta da kaso 200 a zangon karatu na 2022/2023 a wata sanarwar da ta fitar a Disambar 2022.

Domin rage radadin biyan kudin a lokaci guda, jami'ar ta ba da damar yin biya biyu na kaso 60 da kaso 40 a kowani zangon karatu.

Ta kuma sanar da yiwa yaran ma'aikatanta ragi.

Jami'ar Maiduguri (UNIMAID)

Jami'ar Maiduguri ta ce ta kara kudin makarantarta saboda hauhawan farashin kayayyaki a kasar. Kalli rabe-raben sabon kudin makarantar kamar yadda jami'ar ta sanar a kasa:

  • Sabbin daliban likitanci (Medicine) - N252,500
  • Sabbin daliban fannin gwaje-gwajen likitanci da jinya (Medical Laboratory and Nursing) - N136,500
  • Sabbin dalibai masu karantar fannin sanin sassan jiki (Anatomy) - N162,500
  • Sabbin daliban bangaren kula da motsa jiki (Physiotherapy) - N131,500
  • Sabbin daliban bangaren daukar hoton abun da ke gudana a cikin jikin dan adama (Radiography) - N133,500
  • Tsoffin dalibai a bangaren Makarantar kimiyya da kimiyyar lafiya (Faculty of Basic and Medical Sciences) - Tsakanin N112,000 da N258,000

Jami'ar tarayya, Lafia (FULafia)

An rahoto cewa jami'ar tarayya, Lafia, jihar Nasarawa, ta kara kudin rijistan dalibai zuwa N150,000 na wasu bangarorin.

Daliban da ke karanatar bangaren likitanci za su biya N150,000 kudin rijistar sashe.

A halin da ake ciki, kudin rijistan baya cikin kudin makarantar da daliban za su biya.

Jami'ar Uyo (UniUyo)

Dalibai masu dawowa a jami'ar Uyo suna biyan N50,000 a baya. Sai dai kuma a yanzu an kara kudin zuwa fiye da N100,000.

Sabbin daliban likitanci za su biya N105,750, yayin da daliban likitanci masu dawowa za su biya N107,750.

Sabbi da tsoffin dalibai na bangaren ilimi za su biya N75,750 da N77,750 kowannensu.

Dalibai masu dawowa a bangaren kimiyya za su biya N107,750, yayin da sabbin dalibai za su biya N105,750.

Jami'ar karatun noma na Michael Okpara, Umudike

Jami'ar karatun noma na Michael Okpara, Umudike ma ta kara kudin makarantarta, inda ta daura alhakin a kan tsadar gudanar da abubuwa.

Jami'ar ta sanar da ci gaban ne a watan Disambar 2022.

A wani labarin, gwamnatin tarayyar Najeriya ta tura motocin da za su kwashe daliban Najeriya da suka makale a yakin Sudan inda za su kwashe su zuwa kasar Masar inda daga nan za su dawo gida Najeriya a jirgin sama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel