Jama’a Sun Shiga Mamaki Bayan Ganin Gidan Cin Abincin da Ke Amfani da Mutum-Mutumi

Jama’a Sun Shiga Mamaki Bayan Ganin Gidan Cin Abincin da Ke Amfani da Mutum-Mutumi

  • Wani bidiyon da ke nuna cikin wani gidan cin abinci da mutum-mutumi ya ba dan Najeriya abinci ya karade duniyar Instagram
  • A cikin bidiyon, an ga lokacin da mutum-mutumin ya dauko abinci ya kawo wa mutumin da ke zaune kan teburi yana jira
  • Da aka kawo masa abincin, mutumin ya yi murmushi tare da kokarta rungumar na’urar mai fasaha da iya gane mutane

Wani bidiyon da ya nuna yadda mutum-mutumi ke aikin kawo abinci a gidan cin abinci ya jawo cece-kuce game da makomar ayyuka da sana’o’i a karni na 21.

A bidiyon da @tundednut ya yada, mutumin da ya sayi abinci ya nuna farin ciki da karbar cimarsa daga hannun na’ura, ganin yadda mutum-mutumin ya gane shi ba tare da taimakon kowa ba.

Bayan kawo abincin, mutum-mutumin ya yi tafiyarsa nan da nan, mutumin da aka ba abincin kuwa yana ta mamaki, har da daga masa hannu.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Wani gini ya ruguje a barikin 'yan sanda, ya kashe, ya danne mutane da yawa

Yadda mutum-mutumi ke aikin dan Adam a otal
Lokacin da mutum-mutumi ke hidima a otal | Hoto: @tundednut
Asali: Instagram

Mutane da yawa da suka ga mutum-mutumin sun bayyana damuwar cewa, akwai yiwuwar irin wadannan na’urori a gaba su maye gurbin wasu mutanen.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shi kansa wanda ya yada bidiyon a Instagram abin da ya fada kenan, inda yace dubban mutane a Najeriya da basu da sana’a za su so yin aikin da wannan na’urar ke yi cikin farin ciki.

Kalli bidiyon a nan:

Martanin jama’a

@yuuriavvuiLCJay yace:

"Tunani nake ranar da mutum-mutumin zai ci abinci na... za ku gane ni ne Zazoo kuma ina rayuwa ne gidan dambobi.”

@officialmorientez yace:

"Tunani nake ya dauki abinci na ya kai wani teburin a ranan zai ga hauka.”

@ijoba101 ya rubuta:

"Meye yasa mutum-mutumin bai dauki abincin ya ajiye a kan teburi ba tunda yana da hankali.”

Yadda ‘yan Najeriya suka yi amfani da wayoyin hannu da kuma ‘data’ a bara

Kara karanta wannan

Hakimin mata: Mata ta gano mijinta zai kara aure, ta yashe kudin asusun hadin gwiwarsu

A wani rahoton da muka kawo muku, an bayyana adadin amfani da wayoyin salula da aka yi a Najeriya a watanni uku na karshen shekarar 2022 da ta gabata.

Rahoton ya bayyana cewa, an fi yin kiraye-kirayen waya da kawa shafukan intanet a jihohin Kano, Legas da Ogun a cikin watannin.

Hakazalika, rahoton ya bayyana layin da aka fi yin amfani dashi da kuma jihohin da su ne na baya wajen amfani da fasahar kira da amfani da yanar gizo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.