Zulum Ya Tausayawa Talaka, Ya Roki Gwamnatin Tarayya Ta Rage Kudin Jami’a

Zulum Ya Tausayawa Talaka, Ya Roki Gwamnatin Tarayya Ta Rage Kudin Jami’a

  • Babagana Umara Zulum ya shiga cikin masu neman a rage kudin karatu a jami’ar Maiduguri
  • Da suka ziyarce shi da idi, Mai girma Gwamnan jihar Borno ya roki shugabannin jami’ar su sake tunani
  • Farfesa Zulum ya nuna mutane su na kokawa a kan yadda aka tsaulawa kudin karatu UNIMAID

Borno - Babagana Umara Zulum ya yi kira ga shugabannin jami’ar Maiduguri da ke jihar Borno, da su janye sabon karin kudin karatu da suka yi.

Rahoton da aka fitar a Leadership ya nuna Mai girma Babagana Umara Zulum ya yi wannan kira ne domin a tausayawa marasa karfi da ke karatu.

Sannan Farfesa Babagana Zulum yana ganin idan aka rage kudin makarantar, hakan zai saukakawa wadanda rikicin yakin Boko Haram ya auka masu.

Gwamnan ya yi wannan kira ne yayin da wasu daga cikin shugabannin jami’o’in jihar suka kai masa ziyarar sallah a gidan Gwamnati a Maiduguri.

Kara karanta wannan

Zaben Majalisa: An Bar APC Da Ciwon Kai, Mutanen Arewa Maso Yamma Sun Huro Wuta

Gaisuwar karamar sallah

Mataimakin shugaban UNIMAID, Farfesa Mohammed Laminu Mele da Farfesa Umaru Kyari Sandade na jami’ar Jiha ne suka ziyarci Gwamna.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rahoton ya ce a nan ne Gwamna Zulum ya yi amfani da wannan dama wajen kokawa cewa iyaye da-dama sun cire ‘ya ‘yansu daga jami’ar tarayyar.

Zulum
Shehun Borno, Kashim da Zulum a filin idi Hoto: @govborno
Asali: Facebook

Dalili kuwa shi ne sabon kudin da aka fito da shi ya yi yawa, Farfesa Zulum yake cewa mutum fiye da 500 suka kawo masa kuka domin a rage kudin.

“Ina mai matukar sane da kalubalen da jami’a ta ke fuskanta, amma ko N500, 000 za ku ka rika samu daga kowane dalibi, ba za a shawo kan su ba.
Na samu kiraye-kiraye fiye da 500 a kan karin kudin makarantar da aka yi. Ina so in tsoma baki, ina so shugaban jami’a ya ji kukan mutanen Borno.”

Kara karanta wannan

Bayan Kwanaki 33 a Kasar Waje, An Sanar da Lokacin da Bola Tinubu Zai Dawo Najeriya

- Farfesa Babagana Umara Zulum

Jami'o'i sun yaba da Zulum

Farfesa Mohammed Laminu Mele ya ce jami’o’in biyu sun ga dacewar zuwa gaisuwar sallah a gidan Gwamnati bayan an kammala azumin Ramadan.

The Guardian ta rahoto cewa a madadin jami’o’in biyu, Mohammed Mele ya godewa Zulum a game da irin taimakon da yake yi masu a jihar Borno.

Bola Tinubu ya dawo

Idan aka koma siyasa, labari ya zo wasu masu takara a Majalisar dattawa kamar Barau Jibrin da Godswill Akpabio sun yi kus-kus da Bola Tinubu.

Zababben Shugaban kasar ya sa labule da Shugabannin APC na kasa, Abdullahi Adamu da Abubakar Kyari da kuma wasu Sanatocin Legas da Taraba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng