Bidiyon Karamar Yarinya Na Sallah Cikin Natsuwa a Ranar Idi Ya Dauki Hankalin Jama’a

Bidiyon Karamar Yarinya Na Sallah Cikin Natsuwa a Ranar Idi Ya Dauki Hankalin Jama’a

  • Wani bidiyo mai daukar hankali ya nuna lokacin da wata karamar yarinya ke kallon iyayenta na sallah, sai ita ma ta fara binsu
  • A cikin bidiyon, yarinyar bata san ana daukarta ba a kamera, sai kawai ta fara bin yadda ake yin sallar kamar dama ta iya
  • Karamar yarinyar ta daga hannayenta kamar mai addu’a kamar yadda musulmai da yawa ke yi a lokacin addu’a da kuma bayan sallah

A rayuwar yara, suna koyon abubuwa da yawa ne daga kananan shekaru wajen iyaye da manyan da suka girme su; musamman dabi’un yau da kullum.

Yara na kuma koyo daga wasanni, don haka yake da kyau iyaye suke kulawa tare da daura yara kan turba ta gari don tsira duniya da lahira.

Wasu yaran kuma, basu cika maida hankali ga wasu abubuwan da ke da alaka da hankali da ma kawazuci ba a kananan shekaru.

Kara karanta wannan

Matashi Ya Baiwa Mahaifiyarsa Mamaki, Ya Kaita Yawo a Jirgin Sama Don Murnar Zagayowar Ranar Haihuwarta a Bidiyo

Yarinya na sallah
Lokacin da yarinyar ke sallah | Hoto: @muslimnewsnigeria
Asali: Instagram

Sau tari kamar wasa, yara kananan na koyon karatu da warware lissafi mai wahala wanda ke sanyawa su girma masu hazaka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Labarin yarinya mai sallah kamar babban mutum

Wani bidiyon da aka yada na karamar yarinya na yin sallah ya jika zukata, ya kuma dauki hankalin mutane da yawa.

A bidiyon, an ga lokacin da yarinyar ke sallah ba tare da wata matsala ba, alamar da ke nuna ta jima tana kallon yadda ake sallah; watakila daga iyaye.

Tsaf, yarinyar ta yi sallarta dalla-dalla cikin natsuwa kamar yadda babban mutum mai shekaru baligi zai iya yi.

Duk da cewa Legit.ng bata iya gano daga ina bidiyon ya fito ba kuma daga wane gari ne, amma alamu sun nuna a filin sallar Idi ne bayan liman ya idar da sallah.

Wani mai amfani da kafar sada zumunta da ya yada bidiyon ya ce wannan lamari ne mai kyau kuma mai daukar hankali.

Kara karanta wannan

Tir da talauci: An kirkiri motar da mutum zai iya kiranta a waya, kuma ta zo babu direba

Kalli bidiyon:

Kasar Kuwait ta hana amfani da waya wajen sallah

A wani labarin kuma, kunji yadda kasar Kuwait a cikin watan Ramadana ta hana amfani da wayoyin hannu wajen karanta Al-Qur’ani a sallolin dare.

Wannan gargadi ne da aka ba limamai a kasar don ba su damar kiyaye tilawa da haddar littafi mai tsarki da suka yi.

Hakazalika, hakan zai ba jama’a damar daukar littafin a matsayin abu mai ban sha’awa su ma su shajja’a zuwa karanta shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.