Jihohin Najeriya: Inda Aka Fi Yawan Kiran Waya da Amfani Da ‘Data’ a Kasar Nan
- Ofishin kididdiga a Najeriya na NBS ya fitar da rahoton sadarwa da amfani da kayayyakin fasaha a kasar
- An bayyana adadin amfani da wayoyin hannu da aka yi; kama daga kira har zuwa amfani da shafukan sada zumunta
- Hakazalika, an bayyana jihohin da suka fi yawan amfani da wadannan kayayyaki na fasaha da kuma layin da aka fi amfani dashi
Najeriya - Legas, Ogun da Kano ne jihohin da suka fi yawan masu amfani da wayoyin hannu da kuma hawa shafukan intanet, inji ofishin kididdiga na NBS, inji rahoton Business Day.
A rahoton da NBS ya fitar na harkokin tarho, ya kunshi bayanai game da amfani da wayoyi ‘data’ a watanni uku na karshen 2022.
Hakazalika, bayanan sun kunshe adadin masu kiraye-kirayen waya, amfani da shafukan intanet har ma da kamfanonin sadarwar da ‘yan Najeriya ke amfani dasu.
Kididdigar da NBS ya fitar; inda aka fi kira da amfani da ‘data’
Rahoton na NBS ya bayyana cewa, a karshen watanni ukun 2022, ‘yan kasar nan sun yi kiran waya sau 222,571,568. Yawan wadanda suka yi amfani da intanet kuma ya kai 154,847,901.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
1. Jihar Legas
Kiran waya: 26,460,867
Amfani da ‘data’: 18,702,394
2. Jihar Ogun
Kiran waya: 12,994,352
Amfani da ‘data’: 9,206,614
3. Jihar Kano
Kiran waya: 12,373,201
Amfani da ‘data’: 8,470,131
Kididdigar da NBS ya fitar; inda aka suke a kuran baya a kira da amfani da ‘data’
1. Jihar Ekiti
Kiran waya: 2,001,846
Amfani da ‘data’: 1,474,970
2. Jihar Ebonyi
Kiran waya: 1,920,996
Amfani da ‘data’: 1,264,825
3. Jihar Anambra
Kiran waya: 1,571,692
Amfani da ‘data’: 1,101,002
Kamfanin sadarwa na MTN aka fi amfani dashi a Najeriya, inda aka yi kiran da ya kai 89,016,678 da kuma amfani da ‘data’ da ya kai 65,619,610, NairaMetrics ta tattaro.
Alkawura 3 da Buhari ya yi, amma ya gaza cikawa
A wani labarin kuma, mun tattaro muku wasu manyan alkawuran da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taba yiwa ‘yan kasa amma ya gaza cikawa.
A rahoton, an kawo tsaro, tattalin arziki da yaki da rashawa a matsayin abubuwan da Buhari bai tabuka abin da ya kamata da ake tsammani ba.
Sai dai, an yaba wa shugaban kasan wajen cimma nasara a fannin gine-gine da samar da ababen more rayuwa a kasar.
Asali: Legit.ng