Wacce Al’ada Ce Wannan?” Bidiyon Amarya Tana Tuka Tuwo a Wajen Bikinta Ya Yadu
- An gano bidiyon wata kyakkyawar budurwa cikin shiga ta alfarma tana tuka tuwo a kan murhu a ranar aurenta
- A bidiyon, wanda ya ja hankalin masu kallo fiye da 403k a TikTok, an bukaci amaryar da ta tuka tuwo a wajen bikinta
- Alamu sun nuna wannan wata al'ada ce ta mutanenta saboda ta tuka tuwon cikin annashuwa a gaban mutanen da suka taru
Wani bidiyo mai tsawon sananni 22 a TikTok ya nuno wata kyakkyawar amarya tana tuka tuwo a ranar daurin aurenta.
Shafin @kingkayo720 wanda ya dauki hotunan auren shine ya wallafa bidiyon lokacin farin cikin a TikTok.
An dauki amaryar zuwa gaban murhun da aka hada a bainar jama'a da suka hallara a wajen shagalin bikin.
Amarya ta tuka tuwo a kan murhu yayin bikin aurenta
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
An daura wani katafaren tukunya a kan murhu, inda aka dunga zuba garin tuwo a tafasasshen ruwa.
Ta kama dogon muciyar a lokaci guda sannan ta fara tuka tuwon.
Alamu sun nuna hakan na daga cikin al’adunsu saboda ta yi hakan cikin raha yayin da taron jama’a ke ta waka da jinjina mata.
Bidiyon ya ja hankali sosai bayan an wallafa shi a TikTok, inda wasu suka nuna sha’awarsu ga al’adar.
Kalli bidiyon a kasa:
Jama’a sun yi martani
@Chantalwouldgo ya yi martani:
“Haka Afrika take.”
@Precious Gold Precio ya ce:
“Na tayaki murna. Hadadden tufafi.”
@alandratomo ta yi martani:
“Kwarai dole ya kasance haka.”
@user25930869682450 ta yi martani:
“Na so tufafinki.”
@Severine Kana ta yi martani:
“Afrika na da kyau.”
@user4827927241348 ya ce:
“Wacce al’ada ce wannan? Nagode da kuka sanar da ni.”
@esnath08 ya ce:
“Tufafin ya yi kyau.”
A wani labari na daban, mun ji cewa wani matashi ya tashi kan wata kyakkyawar budurwa da ya hadu da ita a wani kantin siyayya a babban birnin tarayya Abuja.
Matashin ya hadu da budurwar ne yayin da take tare da mahaifiyarta inda ya dunkule wata yar wasikar soyayya ya mika mata, dauke da zantuka masu tsuma zuciya.
Hakan ya burge matashiyar har ta kasa boye farin cikin da ke zuciyarta yayin da ta saki kayataccen murmushi.
Asali: Legit.ng