Lokaci Yayi: Najeriya Ta Yi Babban Rashin Gogaggen Dan Jarida

Lokaci Yayi: Najeriya Ta Yi Babban Rashin Gogaggen Dan Jarida

  • Najeriya ta yi rashin babban ɗan jarida wanda ya goge sosai a harkar aikin jarida a gida da wajen ƙasar nan
  • Peter Enahoro ya yi bankwana da duniya ne inda ya koma ga mahaliccin sa yana da shekara 88
  • Enahoro wanda aka fi sani da Peter Pen na daga cikin na farko-farko da suka assasa aikin jarida a ƙasar nan

Birnin Landan - Gogaggen ɗan jarida kuma ɗaya daga cikin ƴan Najeriyan da ake ji da su a fannin aikin jarida, Peter Enaharo, ya koma ga mahaliccin sa.

Jaridar Punch ta kawo rahoto cewa Enahoro, wanda aka fi sani da Peter Pan, ya mutu ne a birnin Landan na ƙasar Burtaniya a ranar Litinin yana da shekara 88 a duniya.

Peter Enahoro ya kwanta dama
Peter Enahoro ya mutu yana da shekara 88 Hoto: Premiumtimes.com
Asali: UGC

Labarin mutuwar ta sa na ƙunshe ne a cikin wata ƴar gajeruwar sanarwa da fitacciyar ƴar jarida mace a ƙasar nan Ms Bunmi Sofola, ta fitar.

Kara karanta wannan

Ana Dab Da Fara Kidaya, Gwamnatin Jihar Arewa Ta Yi Kiran a Dakata, Ta Kawo Dalilanta

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Ina baƙin cikin sanar da mutuwar gogaggen ɗan jaridar mu, Peter Enahoro 'Peter Pan' yau a birnin Landan yana da shekara 88 a duniya. RIP"
"Wanda aka fi sani da sunan 'Peter Pan' saboda rubutun sharhin da ya ke yi a mujallar New African da sunan. Ya zama babban ɗan jarida daga nahiyar Afrika wanda aka fi sani a duniya."

An haife shi a ranar 21 ga watan Janairun 1935, Enahoro ya kasance ɗan jarida ne, mawallafi, ɗan kasuwa sannan mai buga littattafai, cewar rahoton Premium Times.

Enahoro yana daga cikin waɗanda suka assasa harkar watsa labarai a Najeriya inda ya zama editan Daily Times yana da ƙananan shekaru.

Marigayin ya yi karatu a makarantar gwamnatin tarayya ta Ughelli, cikin jihar Delta ta yanzu. Sannan ya yi zamani tare da farfesan turanci na farko a nahiyar Afirika, JP Clark.

Kara karanta wannan

Masha Allah An Fara Jigilar 'Yan Najeriya Da Suka Makale a Sudan, Yau Za a Kwaso Da Dama

Alkalin Babbar Kotun Jihar Kwara, Oyinloye, Ya Rasu

A wani labarin na daban kuma, Allah ya yi wa alƙalin babbar kotun jihar Kwara rasuwa. Allah ya karɓi rayuwar alƙalin yana da shekara 58 a duniya.

Mai shari'a Sikiru Adeyinka Oyinloye ya rasu ne bayan ya yi fama da wani ciwon wuya wanda ya ƙi ci ya ƙi cinyewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng