An Samu Karin Wasu 'Yan Matan Chibok Da Suka Tsero Daga Hannun Boko Haram

An Samu Karin Wasu 'Yan Matan Chibok Da Suka Tsero Daga Hannun Boko Haram

  • Bayan kwashe shekaru a tsare a hannun mayaƙan Boko Haram, wasu ɗaliban Chibok sun arce daga hannun ƙungiyar
  • Ɗaliban mata guda biyu sun samu nasarar tserewa ne bayan sojoji sun ƙara ƙaimi wajen yin luguden wuta ga ƴan Boko Haram
  • Sai dai har yanzu akwai sauran ɗalibai da dama da ƙungiyar ke tsare da su tun bayan sace su a shekarar 2014

Jihar Borno - An samu ƴan mata mutum biyu daga cikin ɗaliban makarantar sakandiren kwana ta Chibok a jihar Borno, da suka sake gudowa daga hannun mayaƙan ƙungiyar ta'addancin nan ta Boko Haram.

Shekara 9 da suka gabata mayaƙan Boko Haram sun kutsa har cikin makarantar sakandiren inda suka yi awon gaba da ɗalibai da yawa.

Daliban Chibok 2 sun tsere daga hannun Boko Haram
Dalibai 2 da suka sake tserowa daga hannun Boko Haram Hoto: Aminiya.com
Asali: UGC

Jaridar Aminiya tace ingantattun majiyoyin tsaro da mazauna jihar sun tabbatar da cewa ƙara tsananta luguden wuta da jami'an soji suke yi kan maɓoyar ƙungiyar ya sanya ƴan matan suka samu damar tserowa daga dajin Sambisa.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Bayan Shekaru 2, Ɗaliban FGC Yauri Sun Kubuta Daga Hannun Yan Bindiga

Wata majiya daga fannin tsaro ta bayyana sunan ɗaliban da suka tsero a matsayin Hauwa Mutah da Esther Markus.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Majiyar ta ci gaba da cewa:

"Ɗaya daga cikin ƴan matan ƴar ƙauyen Chibok ce, sannan ɗayar kuma ta fito ne daga ƙauyen Dzilang."

Har yanzu akwai sauran ɗaliban da suka rage a hannun Boko Haram

Ɗaliban makarantar Chibok 96 ne suka yi saura a hannun ƴan Boko Haram da suka sace sun watan Afirilun 2014.

Sati biyu da suka wuce, rundunar soji ta Operation Hadin kai, wacce ke fafata yaƙi da mayaƙan ƙungiyar ta sanar da cewa akwai sauran ɗaliban Chibok 98 da suka rage a hannun Boko Haram.

Kwamandan ɓangaren leken askri na rundunar Operation Hadin Kai, Kanar Obinna Ezuipke ya bayyana cewa:

"Daga cikin ɗalibai 276 na makarantar sakandiren Chibok da aka ɗauke, a shekarar 2014 guda 57 sun tsero, a shekarar 2018 an sako guda 107."

Kara karanta wannan

Rikicin Sudan: Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Dalilin Da Ya Sanya Ta Kasa Kwaso 'Yan Najeriya

"An ceto wasu ɗalibai 3 a shekarar 2019 da wasu ɗalibai 2 a shekarar 2021 sannan aka ceto wasu mutum 9 a shekarar 2022, hakan ya sanya sun zama 178, saura ɗalibai 98 suka yi saura a hannun ƴan ƙungiyar."

'Yan Sanda Sun Gano Masu Shirin Kai Hari Majalisar Dokokin Plateau

A wani rahoton na daban kuma, ƴan sanda sun samu nasarar bankaɗo shirin wasu masu son kai hari majalisar dokokin jihar Plateau.

Masu son kai harin na da manufar haddasa rikici a majalisar dokokin jihar wacce ke fama da rikicin shugabanci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng