Kungiyar Yan Yankin Tsakiyar Najeriya Ta Bayyana 'Abu Ɗaya' Da Zai Iya Saka Yan Najeriya Su Yafe Wa Buhari

Kungiyar Yan Yankin Tsakiyar Najeriya Ta Bayyana 'Abu Ɗaya' Da Zai Iya Saka Yan Najeriya Su Yafe Wa Buhari

  • Ana cigaba da cece-kuce tun bayan da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nemi yafiyar yan Najeriya a shirye shiryen barin ofis ranar 29 ga watan Mayun 2023
  • Kafin bikin mika mulki ga zababben shugaban kasa, Bola Tinubu, Buhari a ranar Juma'a, ya roki yan Najeriya da ya bata wa rai a tsawon shekara takwas, da su yafe masa, amma hakan bai yi dadi ga yan Najeriya ba
  • Da take martani kan batun, kungiyar Middle Belt Forum ta jaddada cewa abu daya da zai sa yan Najeriya su yafe wa Buhari shine idan ya gyara "kuskuren da hukumar INEC ta yi ya kuma mika mulki ga mutanen da suka dace ba mutanen banza ba"

Yan Najeriya na cigaba da martani ga kalaman Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na neman yafiya, a shirye shiryen sauka daga mulki da kuma mika mulki ga zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Tinubu, ranar Litinin, 29 ga Mayun 2023.

Kara karanta wannan

Babu Murdiya, Babu Magudi – Minista Ya Ambaci Silar Nasar Tinubu a Zaben 2023

Kungiyar mutanen Yankin Tsakiyar Najeriya wato Middle Belt Forum, (MBF), da take nata martanin ta bayyana 'abu taya' da zai iya sanya yan Najeriya yafe wa Shugaba Buhari.

Bola Tinubu da Buhari
Kungiyar Middle Belt Forum ta roki Buhari kada ya mika mulki ga mutanen marasa gaskiya. Hoto: Muhammadu Buhari
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Me zai sa yan Najeriya si yafe wa Buhari, Middle Belt Forum ta bayyana

Kungiyar ta ce hanya daya ce kadai ka iya sa yan Najeriya su yafe masa shine idan ya gyara kuskuren da hukumar zabe INEC ta yi, jaridar The SUN ta ruwaito ranar Litinin, 24 ga Afrilu.

Da yake magana kan lamarin, shugaban kungiyar na kasa, Dakta Bitrus Pogu, ya ce,

"idan yana so mu yafe masa, ya gyara kuskuren da hukumar zabe tayi ta yadda zamu samu jagoranci na mutanen da suka dace mu kuma samu irin Najeriyar da muke fata. Kada ya mika mulki ga mutanen banza ya tabbatar ya mika mulki ga wanda ya dace."

Kara karanta wannan

Ku yafe min: Abu 1 za ka yi mu yafe maka, martanin kungiyar Arewa ga Buhari

Rantsar da Tinubu: Buhari ya magantu kan mika mulki ranar 29 ga watan Mayu, ya tura da sako ga zababben shugaban kasa

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce zai tarbi zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a fadar gwamnati ranar Litinin, 29 ga Mayu, yana jaddada cewa ranar mika mulkin ba ta canja ba.

Buhari ya bada tabbacin lokacin da yake gaisuwar sallah karama ga Tinubu ta waya.

Duka su biyu sun yi godiya ga Allah bisa zagayowar ranar da kuma addu'ar walwala da cigaban kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164