Agwagi Sun Sanya Injin Jirgin Saman Kasar Amurka Ya Kama da Wuta a Sararin Samaniya

Agwagi Sun Sanya Injin Jirgin Saman Kasar Amurka Ya Kama da Wuta a Sararin Samaniya

  • Wani jirgin kasar Amurka ya tashi amma ya gamu da tsaikon da ya sanya shi saukar gaggawa saboda kama wuta da ya yi
  • An ruwaito cewa, agwagi ne suka jawo jirgin ya fara ci da wuta, lamarin da ya kai ga saukarsa na gaggauta a Ohio ba tare da shiri ba
  • Ya zuwa yanzu, hukumar filin jirgin saman ta yi bayanin gaskiyar abin da ya faru, ya kuma bayyana musabbanin tashin wutar

Ohio, Amurka - Wani jirgin kasar Amurka na Boeing 737 ya kama da wuta a tsakiyar sararin samariya kafin direbansa ya gaggauta saukar gaggawa a filin sauka da rashin jirage na Ohio.

Rahoto ya bayyana cewa, jirgin ya samu tsaiko ne samakon mamaye shi da wasu gungun agwagwi mai tashi suka yi, rahoton Punch.

Lamarin an ce ya faru ne jin kadan; akalla mintuna 40 bayan da jirgin ya tashi a ranar Lahadi 23 ga watan Afrilun 2020.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Wani gini ya ruguje a barikin 'yan sanda, ya kashe, ya danne mutane da yawa

Jirgin Amurka ya kama da wuta
Lokacin da jirgin ya kama da wuta | Hoto: dailymail.co.uk
Asali: UGC

A cewar rahoton Mail Online, biyu daga cikin fasinjojin jirginl Marni Kallestad da Ryan Brink ne suka dauki bidiyon yadda injinsa ya kama da wuta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daga ina jirgin ya tashi?

Jirgin na American Airline da ya nufi Phoenix a birnin Arizona ya tashi ne daga filin jirgin sama na kasa da kasa na John Glen Columbus da misalin karfe 7:43 na safe, inda ya gaggauta sauka da misalin karfe 8:22 na safe, kamar yadda kafar FlightAware ta nuna.

Wani ganau na yadda jirgin ya smau tsaiko ya ce, jirgin ya gamu ne da wasu tarin agwagi masu tashi a lokacin da ya tashi, wanda hakan ya sanya tartsatsin wuta ya kama a injinsa nan take.

Sai dai, a wani rubutun gyara zance da aka yi a Twitter, hukumar filin jirgin ta ce, an samu matsaloli da ba a rasa ba, amma ba injin ne ya kama da wuta ba.

Kara karanta wannan

Ganduje Ya Gabatar Da Wata Muhimmiyar Bukata 1 Tak Da Yake So Abba Gida-Gida Ya Cika Masa

Jirgi ya fadi a Ukraine

A wani labarin kuma, kunji yadda wani jirgin sama ya fadi a kasar Ukraine, inda ake fargabar ya hallaka yara da yawa ‘yan makaranta.

Lamarin ya faru ne a daidai lokacin da kasar ke ci gaba da fuskantar tashin hankalin farmakin kasar Rasha da ke ci gaba da faruwa.

Ya zuwa lokacin da muka samu rahoto, an ce jirgin ya fadi ne a kan wata makarantar yara da ba a tantance adadin wadanda hadarin ya shafa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.