Ka Gyara Kuskuren INEC Idan Kana So Mu Yafe Maka, Shugaban MBF Ga Shugaba Buhari

Ka Gyara Kuskuren INEC Idan Kana So Mu Yafe Maka, Shugaban MBF Ga Shugaba Buhari

  • Neman afuwar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi daga ‘yan Najeriya gabanin barinsa ofis a ranar 29 ga watan Mayu ya jawo cece-kuce
  • Gabanin mika mulki ga Tinubu, Buhari ya nemi ‘yan Najeriya da su yafe masa idan ya bata musu rai a shekarunsa takwas na mulki
  • Da yake martani ga batun, zauren Middle Belt Forum ya ce, ‘yan Najeriya za su yafe wa Buhari kadai idan ya gyara kwamacalar da INEC ta yi a zaben bana

Najeriya - ‘Yan Najeriya na ci gaba da yin martani ga batun da ya shafi neman afuwar da Buhari ya kafin ya sauka a mulki a ranar 29 ga Mayu ya mika wa Bola Ahmad Tinubu.

Zauren Middle Belt Forun (MBF) da yake martani ga batun Buhari, ya ce ‘yan Najeriya za su yafe masa ne kadai idan ya yi gyara kafin tafiyarsa.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari Ya Cire Tsoro, Ya Faɗi Babban Abinda Ya Yi Nadama A Mulkinsa

A cewar zauren, abu daya da zai faru ‘yan Najeriya su yafe ma Buhari ba komai bane face ya gyara kuskuren da hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta yi a zaben bana.

Abu daya ne zai sa mu yafewa Buhari, inji kungiyar Arewa ta MBF
Shugaban kasa Muhammadu Buhari na Najeriya | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Abin da Buhari zai yi ‘yan Najeriya su yafe masa, kungiyar MBF

Zauren ya ce, ya lura INEC ta yi kuskure a zaben bana, don haka Buharin ya gyara don samun yafiyar ‘yan kasa, kamar yadda jaridar Daily Sun ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da yake magana game da lamarin, shugaban zauren na kasa, Dr, Bitrus Pogu ya ce:

“Idan yana son mu yafe masa, ya gyara kuskuren da hukumar zabe ta INEC ta yi ta yadda za mu samu wanda ya dace a ofishi kuma mu samu irin Najeriyar da muke nema.
“Bai kamata ya mika mulki ga marasa gaskiya ba amma ya tabbatar mutumin da ya dace ya maye kujerar ofishin.”

Kara karanta wannan

29 Ga Watan Afrilu: Buhari Ya Fadi Dalilin Da Yasa Baya Fargabar Mika Mulki

Shugaban kasa ya nemi afuwar ‘yan Najeriya

A tun farko, kunji yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nemi ‘yan Najeriya su yafe masa bisa kuskuren da ya aikata musu a cikin shekaru takwas na mulkinsa.

Ya bayyana a sakonsa na barka da sallah a karamar sallah da aka gudanar a duniya a ranar Juma’a 21 ga watan Afrilu.

Kamalan Buhari sun sanya ‘yan kasar da yawa suna ci gaba da bayyana martani mai daukar hankali game da matsayarsu kan mulkinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.