29 Ga Watan Mayu: Tinubu Da Wasu Yan Najeriya Da Ake Ganin Su Buhari Ke Baiwa Hakuri a Sakonsa

29 Ga Watan Mayu: Tinubu Da Wasu Yan Najeriya Da Ake Ganin Su Buhari Ke Baiwa Hakuri a Sakonsa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a sakonsa na bikin karamar Sallah, ya baiwa wasu yan Najeriya da watakila ya kuntata masu yayin da yake rike da madafun ikon kasar hakuri.

Shugaba Buhari da wasu fitattun yan Najeriya
29 Ga Watan Mayu: Tinubu Da Wasu Yan Najeriya Da Ake Ganin Su Buhari Ke Baiwa Hakuri a Sakonsa Hoto: Femi Adesina, Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Shugaban kasar ya ce:

“Duk wadanda na kuntatawa, Ina mai neman su yafe mani. Ina ganin ya kamata na yi bankwana da ku sannan na gode maku da kuka yi hakuri da ni na kusan shekaru takwas.”

Sai dai kuma, ana ganin rokon da Shugaba Buhari ya yi yana iya zuwa kai tsaye ga wasu manyan yan Najeriya, a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da sauran jam’iyyun adawa.

Ga jerin wasu daga cikin mutanen a kasa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Bola Tinubu

Zababben shugaban kasa, Bola Tinubu, na iya kasancewa daya daga cikin mutanen da Buhari ke ba hakuri a bainar jama’a bayan manufarsa na sauya takardun naira wanda ya kusa lalata damar da Tinubu da APC ke da shi a lokacin zaben shugaban kasa na 2023.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Buhari Ya Fadi Lokacin Da Yan Najeriya Da Ke Zaune a Sudan Za Su Fara Dawowa Kasar

Gabannin zaben fidda gwanin APC, Tinubu ya bugi kirjin cewa ya marawa Buhari baya wajen zama Shugaban kasar Najeriya, amma an yi zargin cewa an sauya kudi ne don kada Tinubu ya ci zabe.

Yemi Osinbajo

Ana ganin mataimakin Shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo na cikin wadanda Buhari ke ba hakuri. An tattaro cewa ya yi biyayya ga shugaban kasar sosai sannan yana ta burin cewa Buhari zai saka masa sannan ya mara masa baya a matsayin magajinsa.

Komai ya sauya lokacin da aka rahoto cewa Shugaban kasar ya lamuncewa Ahmed Lawan, Shugaban majalisar dattawa a matsayin dan takarar da APC ta tsayar a ranar zaben fidda gwanin jam’iyyar.

Samuel Ortom

Daya daga cikin gwamnonin da gwamnatin Buhari ta kuntatawa sosai shine Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom. An zabi gwamnan da Buhari a karkashin inuwar APC a 2015 har sai da rikici tsakanin manoma da makiyaya ya barke a jihar.

Kara karanta wannan

To fah: Sanatan APC ya yi fade-fade, ya tono gaskiyar batu game da lafiyar Tinubu

Rikicin ya ci gaba da ta’azzara har ya raba kawunan shugabannin 2 lokacin da Ortom ya fara yi wa kabilar shugaban kasar, Fulani a matsayin bara gurbi a lamarin. Da wuya ya fadi wani abu mai kyau game da shugaban kasar.

Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da matarsa

Daya daga cikin manyan yan Najeriya da watakila Shugaba Buhari ke neman yafiyarsa shine Zakzaky da matarsa, Zeenat, wadanda rundunar sojojin Najeriya ta kama a watan Disambar 2015 sannan aka tsare su tun lokacin.

Babban kotun jihar Kaduna ta saki Shugaban kungiyar na Shi’a amma har yanzu ana tsare da ma’auratan kusan shekaru 8.

Omoyele Sowore

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar African Action Alliance (AAC) na daya daga cikin manyan masu sukar gwamnatin shugaban kasa Buhari sannan aka kama shi da tsare shi ba tare da bin umurnin kotu ba.

A watan Agustan 2019, hukumar SSS ta kama shi sannan ta tsare shi bayan ya nemi ayi zabga-zangar “juyin juya hali”. Jami’an tsaro sun tuhume shi da laifin cin amanar kasa amma kotu ya sake shi, sannan aka sake kama shi.

Kara karanta wannan

29 Ga Watan Afrilu: Buhari Ya Fadi Dalilin Da Yasa Baya Fargabar Mika Mulki

Kallo bidiyon Shugaban kasar yana ba da hakuri a nan:

Gwamna Matawalle ya dawo da sarkin Birnin Yandoto

A wani labari na daban, mun ji cewa gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya dawo da Alhaji Aliyu Garba Marafa a matsayin sarkin Birnin Yandoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng