Kasashen Burtaniya, Saudiyya da Amurka Sun Fara Kwashe ’Yan Kasarsu a Lardin Sudan

Kasashen Burtaniya, Saudiyya da Amurka Sun Fara Kwashe ’Yan Kasarsu a Lardin Sudan

  • Dalibai da gama-garin ‘yan Najeriya da ke zaune a Sudan suna cikin tashin hankali yayin da kasashe suka fara tattara ‘yan kasarsu a kasar
  • Shugaban kasar Sudan Abdel Fattah al-Burhan, ya shawo kai tare da amincewa a debe ‘yan kasar waje da ke zaune a kasa
  • Ya zuwa yanzu, gwamnatin Najeriya bata ce komai ba, yayin da kasashen Saudiyya da Jordan suka fara aikin debe ‘yan kasarsu

Goben dalibai da gama-garin ‘yan Najeriya mazauna Sundan na cikin yanayi mai ban tsoro yayin da ake ci gaba da yaki a Sudan.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, shugaban Sudan kuma kwamadan sojin kasar, Abdel Fattah al-Burhan ya amince a debe ‘yan kasar waje; ciki har da jami’an diflomasiyya da dalibai.

A tun farko, gwamnatin Najeriya ta hannun hukumar kula da ‘yan Najeriya mazauna waje (NIDCOM) ta bayyana cewa, dauko ‘yan Najeriya daga Sudan kusan ba zai yiwu ba saboda yadda ake hare-hare kan filayen jiragen kasar.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Inda Aka Kwana Kan Batun Kwaso Yan Najeriya Daga Sudan

Halin da daliban Najeriya ke ciki a Sudan
NIDCOM ta ce akwai matsala wajen kwashe 'yan Najeriya a Sudan | Hoto: Abike Dabiri-Erewa
Asali: UGC

Wani rahoton Punch ya naqalto wani yankin sanarwar da ke cewa, farmakin da ake kai wa kan filayen ya kai ga an kone wasu jirage.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Biyo bayan bayanin shugaban kasa, dalibai da ‘yan Najeriya mazauna na sa ran gwamnatin Najeriya ta sake duba matsayarta.

Saudiyya da Jordan sun sanar da fara tattara ‘yan kasarsu

Wata sanarwa daga kakakin shugaban Sudan ta tabbatar da cewa, kasashen Amurka, Burtaniya, Faransa da China sun fara debe ‘yan kasarsu daga birnin Khartoum.

Ya bayyana cewa, zai mutunta yarjejeniya da kuma tabbatar da kwashe ‘yan kasashen waje kamar yadda gwamnatin Sudan ta yi alkawari.

Hakazalika, an tabbatar da cewa, kasasr Saudiyya ta kwashe ‘yan kasarta yayin da kasar Jordan za ta kwashi nata ‘yan kasar a ranar Asabar.

Sakon shugaba Buhari kan yakin da ake a Sudan

Kara karanta wannan

Binciken ‘Yan Majalisa Ya Jefa Wasu Ministoci a Matsala, An Fito da Zargin $200m

A wani labarin, kunji yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga a tsakaita wuta bayan da rikici ya barke tsakanin sojin kasar da ‘yan tawaye.

Shugaban ya ce, wannan yakin da ya fara a kasar ba abin so bane, inda yace ya kamata a nemi mafita don warware duk wata matsala.

Hakazalika, Buhari ya yi Allah wadai tare da kiran wannan rikicin da ya fara da babban abin takaicin da bai kamata ya ci gaba da faruwa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.